Koma ka ga abin da ke ciki

Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa?

Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa?

Mece ce amsarka?

  • E.

  • A’a.

  • Wataƙila.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

“Za a yi tashin matattu.”—Ayyukan Manzanni 24:15, Littafi Mai Tsarki.

ABIN DA ZA KA IYA MORA IDAN KA GASKATA DA HAKAN

Za ka more ta’aziya sa’ad da aka yi maka rashi.—2 Korintiyawa 1:3, 4.

Ba za ka ji tsoron mutuwa ba.—Ibraniyawa 2:15.

Tabbataccen begen sake ganin ƙaunatattunka da suka mutu.—Yohanna 5:28, 29.

ZA MU IYA GASKATA DA LITTAFI MAI TSARKI KUWA?

Hakika, aƙalla saboda waɗannan dalilai uku:

  • Allah ne Mai ba da rai. Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ne ya “ba kowa rai.” (Ayyukan Manzanni 17:24, 25; Zabura 36:9) Wanda ya halicci dukan abubuwa masu rai yana da ikon sake rayar da mutumin da ya mutu.

  • Allah ya ta da matattu a dā. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labaran mutane takwas, yara da manya, maza da mata waɗanda aka ta da su daga matattu a nan duniya. Wasu a cikin su sun mutu na wasu ’yan sa’o’i ne kawai kafin aka ta da su, amma akwai wanda ya yi kwana huɗu a mace!—Yohanna 11:39-44.

  • Allah yana ɗokin sake ta da matattu. Jehobah ya tsani mutuwa; yana mata kallon magabciya. (1 Korintiyawa 15:26) Yana “marmarin” kawo ƙarshen wannan magabciyar ta wajen ta da matattu. Yana ɗokin ta da waɗanda suka mutu don su sake rayuwa a duniya.—Ayuba 14:14, 15.

KA YI TUNANI A KAN WANNAN TAMBAYAR

Me ya sa muke tsufa da kuma mutuwa?

Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar a FARAWA 3:17-19 da kuma ROMAWA 5:12.