Koma ka ga abin da ke ciki

HALITTARSA AKA YI?

Yadda Aka Tsara Hakoran Wani Irin Dodon Kodi Mai Suna Limpet

Yadda Aka Tsara Hakoran Wani Irin Dodon Kodi Mai Suna Limpet

 Wannan dodon kodi da ake kira Limpet da ke zama a ruwa yana da hakora masu karfi sosai fiye da na sauran halittu. Hakoran sun kunshi kananan zaren karfe da aka saka a sinadarin furotin mai laushi.

 Ka yi la’akari da wannan: Bakin wannan kodin yana cike da hakora kuma hakoran kanana ne sosai. Kowane hakori yana da karfi sosai, kuma shi ne yake taimaka masa ya iya kankare abinci daga jikin duwatsu.

 Masana sun yi amfani da madubi mai kara girma mai karfi sosai don su gwada irin karfin da hakoran suke da shi. Sun gano cewa hakoran wannan kodi sun fi dukan abubuwan da suka gwada karfi har da yanar gizo. Shugaban masu yin binciken ya ce: “Ya kamata mu kwaikwayi yadda tsarin bakin wannan kodi yake don kera abubuwa.”

 Masana sun gaskata cewa za a iya yin amfani da abubuwan da aka kera hakoran wannan kodin, don a kera motoci da jiragen ruwa da jiragen sama da kuma gyara hakoran ’yan adam.

 Mene ne ra’ayinka? Kana ganin cewa yadda hakoran wannan kodi yake sakamakon juyin halitta ne? Ko akwai wanda ya halicce shi?