Koma ka ga abin da ke ciki

TAIMAKO DON IYALI

Sa’ad da Ra’ayi Ya Bambanta

Sa’ad da Ra’ayi Ya Bambanta

 Da yake halaye da kuma abubuwan da mata da miji suke so ya bambanta, hakan yana iya jawo matsaloli. Za su iya fama don su magance matsaloli kamar:

  •   Yawan lokaci da za a rika ziyartar dangin

  •   Yadda za a yi amfani da kudi

  •   Batun haifan yara

 Me za ka iya yi idan ra’ayinka da na matarka ya bambanta?

 Abin da ya kamata ka sani

 Don kun dace da juna, hakan ba ya nufin cewa za ku kasance da ra’ayi daya. Ra’ayin mata da miji da suka dace da juna sosai zai iya bambanta a wasu batutuwa, har ma da batutuwa masu muhimmanci.

 Wata mai suna Tamara ta ce: “Na yi girma a iyalin da ke son kasancewa tare sosai. A karshen mako, mukan ziyarci kakanninmu da kannen babanmu da mamarmu da yaransu. Amma Iyalin maigidana ba sa yin hakan. Saboda haka, ra’ayinmu ya bambanta a batun ziyartar iyalai da yin magana da danginmu da suke nesa.”

 Wani mai suna Tyler ya ce: “Ra’ayina da na matata bai jitu ba a batun kashe kudi. Saboda haka, bayan ’yan watanni da aurenmu, mun yi gardama a kan batun. Mun tattauna sosai kafin muka sasanta wannan batun.”

Zai iya yiwuwa mutane biyu su kalli wani abu amma su kasance da ra’ayin da ya bambanta. Hakazalika, mata da miji suna iya kasancewa da ra’ayin da ya bambanta a kan wani batu

 Wasu matsalolin ba a magance su ko da an yi sadaukarwa. Alal misali, idan daya daga cikin suruki ko surukuwa na rashin lafiya kuma ana bukatar kula da ita kuma fa? Idan mijin ko mata na son haihuwa amma dayan bai yarda da hakan ba kuma fa? a

 Wani mai suna Alex ya ce: “Ni da matata mun dan tattauna a kan batun haihuwa. Tana tunani sosai a kan wannan batun, amma ra’ayinmu ya bambanta. Ban ga alama cewa za mu iya sasantawa ba.”

 Don ra’ayinku ya bambanta, hakan ba ya nufin ba za ku yi nasara ba. Wadansu kwararru sun ce za ku iya yin abin da kuka ga dama sa’ad da ra’ayinku bai jitu ba, ko da hakan zai sa ku kashe aurenku. Amma irin wannan ra’ayin na nuna cewa mutum ya fi mai da hankali ga yadda yake ji ne kawai kuma yana raina alkawarin da ya yi wa Allah cewa zai manne wa matarsa ko da me ya faru.

 Abin da za ka iya yi

 Ku kudiri niyyar cika alkawarin da kuka yi. Idan kuka yi haka, za ku kasance da hadin kai, kuma ku iya magance matsalolinku.

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Abin da Allah ya hada, kada wani ya raba.”​—Matiyu 19:6.

 Ku yi la’akari da wannan. Alal misali, a ce daya cikin ma’auratan na son haihuwa amma dayan ba ya so. Akwai abubuwan da ya kamata su yi la’akari da su. Abubuwan sun kunshi:

  •   Yadda dangantakarku take da danko

     Yadda za ku iya daukan nauyin rainon yaro

  •   Hakkin da ke tattare da zama mahaifi ko mahaifiya.

     Akwai abubuwan da suka fi tanadin abinci da kaya da kuma masauki muhimmanci.

  •   Muna da isashen kudi?

     Za ku iya daidaita aikinku da iyali da kuma wasu ayyuka?

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Idan wani daga cikinku yana so ya yi gini, zai fara zauna, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna.”​—Luka 14:28.

 Ka sake mai da hankali ga batun da kyau. Watakila za ku iya magance wasu abubuwa da ke jawo jayayya. Alal misali, idan batun haifan yara ne, mata ko miji da ba ya so su haihu zai iya tambayar kansa ko kanta cewa:

  •   ‘Shin, sa’ad da na ce ba na so mu haihu, ina nufin cewa ba za mu taba yin hakan ba ne ko kuma mu dan dakata ne kawai?’

  •   ‘Ina jinkiri hakan domin ina ganin cewa ba zan iya zama mahaifi ko mahaifiya nagari ba?’

  •   ‘Ina ji tsoro ne cewa mijina ko matata za ta yasar da ni?’

 Wanda ke son haihuwa na iya yin la’akari da wadannan tambayoyin:

  •   ‘Muna a shirye daukan hakkin da ke tattare da zama mahaifi ko mahaifiya?’

  •   ‘Shin, muna da isashen kudin da za mu yi renon yaro da shi?’

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Hikimar da take daga Allah, . . . mai saukin kai ce.”​—Yakub 3:17.

 Ku mai da hankali da abin da ke da amfani a ra’ayin juna. Hakika, zai iya yiwuwa mutane biyu su kalli wani abu amma su kasance da ra’ayin da ya bambanta. Hakazalika, mata da miji suna iya kasancewa da ra’ayin da ya bambanta a kan wani batu. Alal misali, batun yadda za su rika kashe kudi. Kafin ku tattauna wani batu da kuke da ra’ayin da ya bambanta, ku fara da wadanda ra’ayinku ya jitu. Kamar su:

  •   Wane makasudai ne kuka amince da su?

  •   Ta yaya za mu amfana daga ra’ayin juna?

  •   Domin ku rika farin ciki a aurenku, zai yiwu mutum daya ko kuma ku biyu ku daidaita ra’ayinku?

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kada ka yi wa kanka kadai abu mai kyau, amma ka yi wa dan’uwanka kuma.”​—1 Korintiyawa 10:24.

a Ana bukata a tattauna batutuwa masu muhimmanci kafin a yi aure. Duk da hakan, batutuwa na iya tasowa ba zato ba tsammani ko kuma ra’ayi daya daga cikin ma’auratan na iya canjawa a kwana a tashi.​—Mai-Wa’azi 9:11