Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Idan Abokina Ya Bata Mini Rai Kuma Fa?

Idan Abokina Ya Bata Mini Rai Kuma Fa?

 Abin da ya kamata ka sani

  •   Babu wata dangantaka tsakanin ’yan Adam da ba a samun matsala. Da yake abokinka ajizi ne, har ma da wanda ka ke ganin cewa amininka ne yana iya yi ko kuma fadin abin da zai bata maka rai sosai. Kai ma ajizi ne kuma watakila kana iya tuna wani lokaci da ka yi abin da ya bata ma wani rai.—Yaƙub 3:2.

  •   Yana da sauki a bata wa mutum rai a intane. Alal misali, wani matashi mai suna David ya ce: “Idan mutum yana intane kuma ya ga hotunan abokinsa a wurin liyafa, hakan yana iya sa mutumin ya soma tunani dalilin da ya sa ba a gayyace shi ba. Hakan yana iya sa ka ji an ci amanar ka ko kuma ya sa ka bakin ciki.”

  •   Kana iya koyan yadda za ka magance matsalar.

 Abin da za ka iya yi

 Ka binciki kanka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ka zama mai saurin fushi, gama wawa ne mai cike da fushi.”—Mai-Wa’azi 7:9.

 Wata matashiya mai suna Alyssa ta ce: “A wasu lokuta, sai bayan wani dan lokaci za ka fahimci cewa abin da ya bata maka rai bai taka kara ya karya ba.”

 Ka yi tunani a kan wannan: Shin karamin abu yana saurin bata maka rai ne? Kana iya hakura da kurakuran wasu kuwa?—Mai-Wa’azi 7:21, 22.

 Yadda za ka amfana idan kana gafartawa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ƙyale laifi . . . abu ne mai” kyau.—Karin Magana 19:11.

 Wani matashi mai suna Mallory ya ce: “Ko da a ce an bata wa mutum rai sosai, zai fi dacewa mutum ya rika gafartawa. Hakan yana nufin cewa mutum zai mance da laifin da aka yi masa kuma ba zai rika ta da batun a duk lokacin da ya hadu da wanda ya bata masa rai ba. Idan mutum ya gafarta wa wanda ya yi masa laifi yana bukatar ya mance da batun gaba daya.”

 Ka yi tunani a kan wannan: Batun yana da muhimmanci ne sosai? Shin za ka iya yafewa domin ku yi zaman lafiya?—Kolosiyawa 3:13.

Ta da batun da ya jawo sabani tsakaninka da abokinka yana kamar bude kofa a kai a kai don iska mai sanyi ta shiga daki mai dumi a lokacin sanyi

 Ka yi la’akari da yanayin mutumin. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku kula da kanku kaɗai, amma ku kula da waɗansu kuma.”—Filibiyawa 2:4.

 Wata matashiya mai suna Nicole ta ce: “Idan kai da abokinka kuna kauna da kuma daraja juna, hakan zai sa ku nemi hanyar sasanta matsalarku domin dukanku kuna so ku ci gaba da abokantakarku. Kun riga kun kokarta cikin dangantakarku kuma ba za ku so ta yi tsami ba.”

 Ka yi tunani a kan wannan: Shin akwai wani abin da abokinka ya fada da yake da muhimmanci?—Filibiyawa 2:3.

 Gaskiyar al’amarin: Idan ka koyi yadda za ka rika magance abubuwan da ke bata maka rai za ka amfana idan ka girma. Zai dace ka koyi hakan yanzu!