TAMBAYOYIN MATASA
In Ba na Jin Annashuwa Fa?
Ba abin da wasu mutane suka tsana kamar a ce ruwan sama ya tsare mutum a gida, ya hana ka fita, ba abin yi kuma ba wurin zuwa. “Wani matashi mai suna Robert ya ce: “A irin wannan yanayin, zan zauna kawai, in rasa abin da zan yi da rai na.”
Ka taba samun kanka a irin wannan yanayin? Idan haka ne, wannan talifin zai taimaka maka!
Abin da ya kamata ka sani
Yin amfani da na’urar zamani ba zai taimaka maka ba.
Yin amfani da intane zai iya taimaka maka ka dan kashe lokaci, amma kuma zai iya gurgunta zurfi tunaninka ya kuma kara maka rashin jin annashuwa. Jeremy, mai shekara 21 ya ce: “Za ka ga cewa kana kallon na’urar amma kuma hankalinka ba ya wurin.”
Wata budurwa mai suna Elena ta yarda da hakan. Ta ce, “Ba dukan abubuwa ba ne za ka iya yi da na’ura. Zai janye hankalinka daga abubuwa masu muhimmanci, da zarar ka ajiye na’urar, za ka fi jin rashin annashuwa!”
Hali shine mutum.
Shin yawan abubuwan yi zai sa ka ji annishuwa ne? Kome ya dangana ga yadda ka ke sha’awar abin da ka ke yi. Alal misali, wata budurwa mai suna Karen ta tuna kuma ta ce: “Ba na jin dadin makaranta, ko da yake ina da abubuwan yi a makaranta. Dole ne mutum ya shaku a abin da yake yi in ba haka ba ba za ka ji annashuwa ba.”
Ka sani? “Rashin abin yi” ba hujja ba ce amma wani zarafi ne—yanayin yana kama da kasa mai inganci da mutum zai iya yin shuki.
Abin da za ka iya yi
Ka kara yawan abubuwan da za ka so ka dinga yi. Ka nemi sabon abokai. Ka soma yin wani abin da za ka ji dadinsa. Ka yi bincike akan wasu sababbin batutuwa. Mutanen da ke yawan yin abubuwa dabam dabam ba za su ji rashin annishuwa ba yayinda su ke nan su kadai—ko kuma suke tare da wasu!
Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Dukan abin da hannunka ya iske na yi, ka yi shi da karfinka”—Mai Wa’azi 9:10.
Wata mai suna Melinda ta ce: “Bai dade da na fara koyon yaren Mandarin na kasar Sin ba, kuma yayinda nake zuwa wurin koyo, na gano cewa lallai fa abubuwa masu kyau sun wuce ni domin ban soma koyon tuntuni ba. Ina jin dadin samun akin yi. Domin yana sa in mai da hankali na a abin da na ke yi kuma in yi amfani da lokaci na yadda ya kamata.”
Ka mai da hankali ga manufarka. Za ka dada sa kuzari cikin abin da ka ke yi idan ka ga cewa abin da ka ke yi yana da amfani. Ba za ka ji kyuyar yin aikin makaranta ba idan ka san manufarsa.
Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Babu abin da ya fi ga mutum . . . ya ji wa ransa dadi cikin aikinsa.”—Mai-Wa’azi 2:24.
Hannah ta ce: “Lokacin da na kusa kamala makaranta, ina karatun tsawon sa’o’i takwas domin dā ma ban yi wani karatu ba. Na ji kyuyan yin haka ne? Ko kadan domin na sa zuciya na in cim ma buri na. Na mai da hankali akan abin da zan cim ma, wato sauke karatu, kuma hakan ya motsa ni sosai.”
Ka yi na’am da abubuwan da ba za ka iya canjawa ba. Ba kome ne za ka ji dadin yi cikin abubuwan da ka ke son yi ba. Ko abokanka na kud da kud ma za su iya kin yin wasu abubuwa da kai, kuma hakan zai sa ka rasa na yi. Ka yi kokari ka kasance da hali mai kyau maimakon barin irin wadannan abubuwa su raunana ka.
Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Mai farin zuciya yana da buki tuttur.”—Karin Magana 15:15.
Ivy ta ce: “Abokiyata ta ce mini in yi kokari in mori lokaci da nake zama ni kadai. Ta ce mini ya kamata in koyi yadda zan iya jin dadin zama ni kadai da kuma sa’ad da nake tare da wasu, domin wannan hali ne mai kyau da ya kamata kowa ya koya.”