TAMBAYOYIN MATASA
Yin Jimaꞌi ta Baki Shi Ma Jimaꞌi Ne?
A wani rahoto da Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta Amurka ta bayar, ta ce sun gana da matasa masu shekaru tsakanin sha biyar da sha tara kuma kusan rabi daga cikinsu sun ce sun taba yin jimaꞌi ta baki. Wata mai suna Sharlene Azam, wadda ta wallafa littafin nan mai suna Oral Sex Is the New Goodnight Kiss ta ce: “Matasa da yawa suna ganin yin jimaꞌi ta baki ba komai ba ne. A nasu raꞌayin, yin jimaꞌi ta baki ba jimaꞌi ba ne.”
Mene ne naka raꞌayin?
Ka amsa tambayoyi na gaba, e ko aꞌa.
Yarinya za ta iya yin ciki idan ta yi jimaꞌi ta baki?
E
Aꞌa
Ana kamuwa da cuta ne idan aka yi jimaꞌi ta baki?
E
Aꞌa
Yin jimaꞌi ta baki, shi ma jimaꞌi ne?
E
Aꞌa
Me gaskiyar lamarin?
Ka gwada amsoshin da ka zaba da wadanda aka bayar a gaba.
Yarinya za ta iya yin ciki idan ta yi jimaꞌi ta baki?
Amsa: Aꞌa. Wannan dalilin ne ya sa mutane suke gani kamar yin jimaꞌi ta baki, bai da illa. Amma hakan, babban kuskure ne.
Ana kamuwa da cuta ne idan aka yi jimaꞌi ta baki?
Amsa: E. Wadanda suke jimaꞌi ta baki, za su iya kamuwa da cutar hepatitis (A ko B), da kuraje da ake kira genital warts da cutar ciwon sanyi (gonorrhea) da cutar herpes, da kanjamau da kuma syphilis.
Yin jimaꞌi ta baki, shi ma jimaꞌi ne?
Amsa: E. Duk wani shaꞌani da mutum zai yi da gaban (alꞌaurar) wani ko wata don gamsar da shaꞌawar yin jimaꞌi, jimaꞌi ne. Wato, yin jimaꞌi kai tsaye, da yin jimaꞌi ta baki, da yin jimaꞌi ta dubura (tsuliya) da kuma yin wasa da gaba ko alꞌaurar wani ko wata, dukansu jimaꞌi ne.
Me ya sa sanin hakan yake da muhimmanci?
Bari mu bincika wasu nassosi da suka yi magana da ta shafi yin jimaꞌi ta baki.
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama wannan shi ne nufin Allah, . . . ku guje wa halin lalata.”—1 Tasalonikawa 4:3.
A duk saꞌad da Littafi Mai Tsarki ya ambata “halin lalata,” hakan ya kunshi duk wani abin da ya shafi taba alꞌaurar wani ko wata don gamsar da shaꞌawar jimaꞌi, idan ba aure ne ya hada su ba. Duk mai yin lalata yana sa Allah ya yi fushi da shi. Ban da haka ma, akwai wasu munanan sakamako da suke bin bayan wannan halin.—1 Bitrus 3:12.
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku guje wa halin lalata! Duk wani zunubin da mutum yake yi bai shafi jikinsa ba, amma mai lalata yana yi wa jikinsa zunubi.”—1 Korintiyawa 6:18.
OYin jimaꞌi ta baki zai iya sa mutum ya kamu da cuta iri-iri kuma ya daina zama abokin Allah. Zai kuma iya sa mutum ya rika jin wani iri. Littafin nan Talking Sex With Your Kids ya ce: “Wadanda suka yi jimaꞌi tun ba su yi aure ba sukan yi da-na-sani ko kuma su ji kamar abokin zamansu ba ya son su da gaske. Hakan na faruwa ko da wane irin jimaꞌi suka yi. Mutum zai iya fama da wadannan matsalolin muddin ya yi jimaꞌi ba bisa kaꞌida ba.”
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya koya muku domin amfanin kanku.”—Ishaya 48:17.
Kana ganin za ka amfana idan ka bi dokar Allah game da jimaꞌi? Ko dai takura ake maka? Ga wani misali da zai taimaka maka ka gano gaskiyar batun. A ce kana tuki a babban titi inda aka saka alamoni da ke nuna wa direbobi iya gudun da ya kamata su yi, da inda ya kamata su bi, da kuma inda ya kamata su dakata. Shin za ka dauka cewa wadannan alamonin suna takura maka ne ko suna kāre ka? Me kake ganin zai faru idan kai da wasu direbobin kuka yi banza da wadannan alamun?
Haka ma da kaꞌidodin Allah, idan ka yi banza da su, za ka girbe abin da ka shuka. (Galatiyawa 6:7) Wani littafi mai suna Sex Smart ya ce: “Idan ka ci gaba da yin abubuwan da ka san ba su dace ba, kana yin banza da abin da ka yi imani da shi, za ka ci gaba da zub da mutuncinka, kuma kai da kanka za ka rika jin ba ka da daraja.” Amma idan ka bi kaꞌidodin Allah, za ka zama mutumin kirki. Ban da haka ma, zuciyarka ba za ta dame ka ba.—1 Bitrus 3:16.