TAMBAYOYIN MATASA
Me Ya Kamata In Sani Game da Wasanni?
Yin wasanni suna iya taimaka maka ko kuma su sa ka cikin matsala. Amma hakan ya dangana a kan irin wasan da kake yi da yadda kake yin su da kuma tsawon lokacin da kake wasannin.
Mene ne amfanin yin wasanni?
Yin wasanni yana kara koshin lafiya. Littafi Mai Tsarki ya ce “wasa jiki tana da amfaninta.” (1 Timotawus 4:8) Wani saurayi mai suna Ryan ya ce: “Yin wasanni yana sa mutum ya kara karfi. Gwamma mutum ya yi wasanni da ya zauna a gida yana wasannin bidiyo.”
Yin wasanni yana sa ’yan wasa su kasance da hadin kai da kamewa. Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da wani kwatanci a kan yin wasa don ya koyar da darasi mai kyau. Ya ce: “Masu-tsere cikin fage duka su kan yi gudu, amma ɗaya ne ya kan karɓi rawani ... Dukan wanda yake ƙoƙari wurin wasa yana daurewa cikin dukan abu.” (1 Korintiyawa 9:24, 25) Mene ne hakan yake nufi? Don su yi wasa bisa ka’idar wasan, ’yan wasa suna bukatar su rika kame kansu kuma su kasance da hadin kai. Wata yarinya mai suna Abigail ta yarda da hakan, kuma ta ce: “Yin wasanni ya sa ina kasancewa da hadin kai da kuma tattaunawa da wadanda nake wasa da su.”
Yin wasanni yana kara dankon abokantaka. Yin wasanni yana sa mutane su kasance tare. Wani matashi mai suna Jordan ya ce: “Ana yin gasa a dukan wasanni, amma idan kun dauka cewa wasa ne kawai kuke yi, yin wasanni hanya ce mai kyau na samun abokai.”
Wadanne hadarurruka ne ke tattare da yin wasa?
Irin wasannin da kake yi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji yana gwada mai-adalci: amma mai-mugunta da mai-son zalunci ransa yana kinsu.”—Zabura 11:5.
Ana yin mugunta sosai a wasu wasanni. Wata matashiya mai suna Lauren ta ce: “Ana bugun mutum a wasan dambe. Tun da bai kamata Kiristoci su yi fada ba, me ya sa za mu ji dadin kallon wasan da ake bugun mutane?”
Ka yi tunani a kan wannan: Shin kana yin wasa ko kallon wasannin da ake mugunta don kana ganin hakan ba zai sa ka zama mai mugunta ba? Idan haka ne, ka tuna cewa Zabura 11:5 ta ce, Jehobah yana kin mai ‘son zalunci,’ ba kawai mai yin hakan ba.
Yadda kake yin wasan. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada a yi kome domin tsaguwa, ko girman kai, amma a cikin tawali’u kowa ya mai da wani ya fi kansa.”—Filibbiyawa 2:3.
Hakika, ana yin gasa a duk wasannin da rukuni biyu suke yi. Amma ba za ka ji dadin wasan ba idan dole ne sai ka ci. Wani matashi mai suna Brian ya ce: “Idan ka iya yin wasa sosai, hakan zai iya sa ka soma yin gasa da wasu. Saboda haka, kana bukatar ka kara zama mai tawali’u.”
Ka yi tunani a kan wannan: Wani matashi mai suna Chris ya ce, “Mukan yi wasan kwallo a kowane mako, kuma ’yan wasa suna jin rauni sosai.” Saboda haka, ka tambayi kanka, ‘Wadanne abubuwa ne suke sa ’yan wasa su rika jin rauni? Mene ne zan yi don in rage jin rauni?’
Yadda kake yin wasan. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku gwada mafifitan al’amura.”—Filibbiyawa 1:10.
Kana bukatar ka rika sa abubuwa masu muhimmanci a kan gaba; ya kamata abubuwan da suka shafi bautarka ga Jehobah su zama na farko a rayuwarka. Yawancin wasanni suna daukan sa’o’i da yawa, ko kana yin wasan ko kuma kallo kawai kake yi. Wata matashiya mai suna Daria ta ce: “Nakan yi jayayya da mahaifiyata a kan yawan lokacin da nake yi wajen kallon wasanni a talabijin, takan ce da na yi wasu abubuwa masu muhimmanci a wannan lokacin.”
Ka yi tunani a kan wannan: Shin kana saurarar iyayenka idan suka ba ka shawara a kan kafa abubuwa da suka fi muhimmanci a rayuwarka? Wata matashiya mai suna Trina ta ce: “Idan ni da ’yan’uwana muka bar yin ayyuka masu muhimmanci kuma muna kallon wasanni, mahaifiyata takan gaya mana cewa ’yan wasan suna samun kudinsu ko mun kalle su ko ba mu yi hakan ba. Sai ta tambaye mu, ‘Amma wane ne yake biyan ku?’ Abin da take nufi shi ne: ’Yan wasan suna da aiki. Amma idan ba mu yi aikin da aka ba mu a makaranta da kuma wasu abubuwa ba, ba za mu iya biyan bukatunmu a nan gaba ba. Mahaifiyarmu tana nufin cewa bai kamata kallon wasanni ko kuma yin wasa ya fi muhimmanci a rayuwarmu ba.”