Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Ta Yaya Zan Rage Nauyin Jikina?

Ta Yaya Zan Rage Nauyin Jikina?

 Ina bukatar in rage nauyin jikina kuwa?

 Wasu matasa sun ce suna so su rage nauyin jiki. Amma . . .

  •   Mutane da yawa sun damu da siffarsu fiye da lafiyar jikinsu. Don su rage nauyin jikinsu, suna kokari su yi wasu abubuwa da suke gani zai sa su rage nauyin jikinsu da sauri. Sukan daina cin abinci ko kuma su sha magunguna na rage jiki. Hakan ba ya taimaka musu kuma a wasu lokuta suna da lahani.

     Hailey ta ce: “Wasu ’yammata sukan ki cin abinci don su rage jiki da sauri. Hakan yana jawo mugun sakamako, kuma yana daukan dogon lokaci kafin su fardado daga barna da hakan ya yi a jikinsu.”

  •   Bai kamata matasa da yawa da suka damu da nauyin jikinsu su yi hakan ba. Nauyin jikinsu yana da kyau, amma don watakila suna gani sun yi kiba sa’ad da suka gwada kansu da tsararsu ko kuma don sun ga rage nauyin jiki da ake daukakawa a dandalin yada labarai.

     Paola ta ce: “Sa’ad da nake ’yar shekara 13 nakan gwada kai da abokaina. Ina ganin za su fi so na idan na rage jiki kamar su, kuma hakan yana nufi zan rame sosai.”

 Amma wasu matasa suna bukatar su rage nauyin jikinsu. Ƙungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya ta ba da rahoto cewa . . .

  •   A fadin duniya, matasa wajen miliyan 340 masu shekaru tsakanin 5 da 19 suna da kiba sosai.

  •   A shekara ta 1975, matasa kashi 4 cikin masu shekaru 5 zuwa 19 suna da kiba sosai. Amma a shekara ta 2016 adadin ya karu da kashi 18.

  •   A yawancin kasashe a duniya, an fi ganin mutane masu jiki sosai fiye da wadanda ya kamata su kara jiki.

  •   An fi ganin mutane masu kiba sosai a kasashen da suke fama da tattalin arziki, ko a iyalai da wasu ba sa samun isashen abinci da ya dace.

 Wace hanya ce ta fi kyau don rage nauyin jiki?

 Wanne ne za ka zaba?

  1.   Kin cin abinci a wani lokaci.

  2.   Ka rika motsa jiki da cin abinci mai kyau.

  3.   Ka sha magunguna da ke rage nauyin jiki.

 Amsar da ta dace: Na biyu ne ya fi kyau: Ka rika motsa jiki da cin abinci mai kyau.

 Kin cin abinci ko kuma daina cin wasu abinci zai iya sa ka rage nauyin jikinka da sauri. Amma yin hakan ba zai taimaka maka ba, kuma za ka sake yin jiki sosai muddin ka koma cin abinci yadda ka saba.

 Amma idan ka kasance da koshin lafiya, za ka rika jin dadin jikinka. Wani likita mai suna Michael Bradley ya ce: “Za ka sami sakamako mafi kyau . . . sa’ad da ka canja salon rayuwarka kuma ka ci gaba da bin sabon tsarin muddar ranka.” * Mene ne yake nufi? Idan kana so ka rage nauyin jikinka, ka canja salon rayuwarka ba irin abinci da kake ci kadai ba.

 Mene ne za ka yi?

 Littafi Mai Tsari ya ce mu “zama masu hankali” kuma hakan ya kunshi yadda muke cin abinci. (1 Timoti 3:11) Ya ce mu guji cin abinci da yawa ainun. (Karin Magana 23:20; Luka 21:34) Ta wajen bin wadannan ka’idodin, ka bi wannan shawarar don ka kasance da koshin lafiya:

  •   Ka koyi abin da za ka yi don ka rika cin abinci yadda ya dace.

     Bai dace ka zama mai tsattsauran ra’ayi don abin da kake ci ba, amma ka koya game da abinci mai kyau zai taimaka maka ka rika cin abinci da ya dace. Kuma cin abinci mai kyau ne zai fi taimaka maka ka rage nauyin jikinka.

  •   Ka rika motsa jiki a kowane lokaci.

     Ka yi tunanin abubuwan da za ka rika yi kullum don ka rika motsa jikinka. Alal misali, maimakon ka rika shigan lif, ka rika hawan matakalar bene. Maimakon ka rika kallon wasan bidiyo kawai, ka yi amfani da wasu lokuta don zagayawa.

  •   Ka rika cin abinci mai kyau maimakon kayan dadi.

     Wata matashiya mai suna Sophia ta ce: “Nakan ajiye ’ya’yan itatuwa da kayan lambu kusa da ni. Hakan yana sa ba na cin kayan dadi.”

  •   Ka rika cin abinci a hankali.

     Wasu mutane suna cin abinci da sauri kuma ba sa sanin lokacin da suka koshi! Saboda haka, ka rika cin abinci a hankali. Ka dan dakata kafin ka debi karin abinci. Za ka ga cewa ba ka jin yunwa yadda kake tsammani.

  •   Ka lura da yawan kuzari da abincin da kake so ka ci zai ba ka.

     Ka karanta abin da aka rubuta a kwalin abinci da kake so ka saya don ka san yawan kuzari da za ka samu a abincin. Abin da zai taimaka maka shi ne sanin cewa lemon kwalba da kayan dadi suna cikin abinci masu yawan sa kuzari kuma suna sa mutum yin jiki sosai.

  •   Ka kasance da daidaita.

     Sara ’yar shekara 16 ta ce: “Akwai lokacin da na dukufa da kirga yawan kuzari da zan samu a abinci. Har ya kai lokacin da idan na ga abinci duk abin da nake tunaninsa shi ne yawan kuzari da ke abinci!” A wasu lokuta, ya kamata ka dan dandana abu mai dadi ko idan za ka sami kuzari da yawa a abincin.

 Shawara: Ka gaya wa likitanka cewa ka damu da nauyin jikinka. Bisa abin da ya binciko game da jikinka da yanayinka, shi ko ita zai taimaka maka ka rika bin salon rayuwa da zai sa ka kasance da koshin lafiya.

^ Daga littafin nan When Things Get Crazy With Your Teen.