Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Mene ne Ra’ayinka Game da Rantsuwar Kin Yin Jima’i Kafin Aure?

Mene ne Ra’ayinka Game da Rantsuwar Kin Yin Jima’i Kafin Aure?

 Mene ne rantsuwar kin yin jima’i kafin aure?

 Rantsuwar kin yin jima’i kafin aure shi ne alkawarin da matasa suke daukawa a rubuce ko da baki cewa ba za su yi jima’i ba sai bayan sun yi aure.

 Rantsuwar kin yin jima’i kafin aure ya yi tashe sosai a tsakanin shekara ta 1990-1999, bayan da kungiyar Southern Baptist Convention da ke Amirka ta yi wani shiri a talabijin mai jigo “True Love Waits” (Kauna ta Gaskiya Ba ta Hanzari). An tattauna muhimmancin bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki da kuma karfafar da wasu matasa suke yi cewa a guji jima’i kafin aure.

 Bayan wannan shirin, an sake yin wani da aka nuna yadda ake rarraba wa mutanen da suka yi wannan rantsuwar zoben azurfa don su rika tunawa da alkawarin da suka dauka.

 Rantsuwar kin yin jima’i kafin aure yana da amfani kuwa?

 Amsar wannan tambayar ta dangana ne ga wanda ka yi wa tambayar.

  •   Wasu ’yan bincike Christine C. Kim da Robert Rector sun ce, “bincike da yawa sun nuna cewa matasa da ke tsakanin shekara 13-19 da suka yi wannan alkawarin, suna rage ko kuma jinkirin yin lalata.”

  •   Wani bincike kuma da makarantar Guttmacher ta yi ya nuna cewa babu bambanci tsakanin “matasan da suka yi wannan ‘rantsuwar’ da wadanda ba su yi ba.”

 Me ya sa ake da bambancin ra’ayi?

  •   Wasu binciken ma sun gwada ra’ayin wadanda suka yi rantsuwar da na wadanda ba su yi ba da ra’ayinsu ba daya ba ne a batun jima’i.

  •   Wasu kuma sun gwada ra’ayin masu rantsuwar da wadanda ba su yi ba da ra’ayinsu daya ne a batun jima’i.

 Me aka gano daga binciken na biyun nan? Wata likita mai suna Dr. Janet Rosenbaum da ta kware a fannin matsalolin matasa ta ce, “ba a ganin bambanci tsakanin matasan da suka yi rantsuwar da wadanda ba su yi ba bayan shekara biyar.”

 Abin da ya fi dacewa

 Mutanen da suka kafa tsarin rantsuwar kin yin jima’i kafin aure ba su da mugun manufa. Amma matsalar ita ce, ba su ambata abin da za su yi don su rike alkawarinsu ba. Dr. Rosenbaum ta ce “da yawa cikin masu rantsuwar ba sa yin sa da gaske. Ya kamata mutum ya guji yin lalata daga zuciyarsa ba don ya saka hannu a wani tsari ba.”

 Littafi Mai Tsarki bai karfafa mutane su yi irin wannan alkawarin ba a rubuce ko da baki, amma ya taimaka musu don “hankalinsu ya horu yau da kullum, su rarrabe nagarta da mugunta.” (Ibraniyawa 5:14, Littafi Mai Tsarki) Ballantana ma, ba cuta da yin ciki ba ne ya kamata su hana mu yin jima’i kafin aure ba, amma kin yin jima’i kafin aure yana nuna cewa muna girmama Allah wanda ya kafa aure.​—Matta 5:19; 19:4-6.

 Dukan ka’idodin Littafi Mai Tsarki suna da amfani a gare mu. (Ishaya 48:17) Ko da mutum matashi ne ko tsoho, zai iya kudura aniyar bin dokar Allah da ta ce, “ku guje wa fasikanci.” (1 Korintiyawa 6:18) Idan mutum ya yi aure, hakan zai ba shi damar jin dadin jima’a ba tare da damuwa ko kuma yin da-na-sanin da yake tattare da yin lalata ba.