TAMBAYOYIN MATASA
Ta Yaya Zan Rika Bi da Yadda Nake Ji?
Wata mai suna Carissa ta ce: “Yau ina farin ciki gobe ina cike da bakin ciki. Wasu abubuwan da nake ganin kamar ba kome ba ne jiya, suna min wuya in yi a yau.”
Shin, yadda kake ji a zuciyarka yana yawan canjawa kamar yadda ake tafiya a hanya mai gargada? * Idan haka ne, wannan talifin zai iya taimaka maka!
Me yake jawo hakan?
Sa’ad da yaro yake girma kuma yanayin jikinsa yana canjawa, hakan yana iya sa shi yin farin ciki wani lokaci, wani lokaci kuma ya yi bakin ciki. Yaran da suke tsakanin shekara 16 zuwa 19 ma za su iya fama da irin wannan yanayin.
Idan kana samun matsala da yadda kake ji, ka tuna cewa a yawancin lokuta hakan na faruwa ne don canjin yanayin da ke faruwa a jikinka sa’ad da kake girma. Abin farin ciki shi ne, akwai mafita don za ka iya magance irin matsalar idan kana fama da ita.
Gaskiyar ita ce: Sanin yadda za ka bi da matsalar yanzu yana da muhimmanci sosai, daga baya in ka yi girma za ka san yadda za bi da matsaloli dabam-dabam.
Abubuwa uku da za ka iya yi
Ka gaya wa wani. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Aboki kullayaumi kauna yake yi, kuma an haifi dan’uwa domin kwanakin shan wuya.”—Misalai 17:17.
Wata mai suna Yolanda ta ce: “Akwai wata aminiyarmu da nake ganin ta a matsayin antina. Tana kasa kunne sosai idan muna tattaunawa da ita, shi ya sa ba na shakkar gaya mata duk abin da ke dami na. Kuma idan abin da na gaya mata daidai ne sai ta nuna tana alfahari na ni, idan kuma ba daidai ba ne sai ta gaya min abin da zan yi.”
Taimako: Maimakon ka rika gaya wa tsararka matsalolin da kake fuskanta, zai fi ka gaya wa iyayenka ko wani da ya manyanta da ka yarda da shi.
Ka rubuta. Littafi Mai Tsarki ya ce sa’ad da Ayuba yake fama da matsaloli, Ayuba ya ce: “Zan fita da karata a fili; In yi magana cikin bācin raina.” (Ayuba 10:1) Ban da gaya wa wani matsalar da muke fama da shi, za mu iya yin “magana” ta wurin rubuta yadda muke ji.
Wata mai suna Iliana ta ce: “Ina tafiya ko’ina da wani karamin littafi. Idan wani abu ya ban haushi, sai in rubuta abin da ya faru. Rubuta yadda nake ji a littafi yana kama da magani a gare ni.”
Taimako: Ka rika tafiya da littafin da za ka iya rubuta yadda kake ji da abin da ya sa kake jin hakan da kuma yadda za ka bi da yanayin. Shafin rubutu da ke hade da wannan talifin zai taimaka maka ka yi hakan.
Ka yi addu’a. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya taimake ka: Ba za ya yarda a jijjige masu adalci ba.”—Zabura 55:22.
Wata mai suna Jasmine ta ce: “Ina yawan yin addu’a idan ina fama da bakin ciki. kuma a duk lokacin da na gaya wa Jehobah abin da ke zuciyata sai in ji na sami sauki.”
Taimako: Ko da kana fama da bikin ciki, ka yi kokari ka tuna abubuwa uku da kake so ka yi godiya a kai. Sa’ad da kake addu’a, ka roke Jehobah ya taimaka maka amma kar ka manta ka gode masa don abubuwan da ya ba ka.
^ A wannan talifin za a tattauna yadda wasu matasa suke ji sa’ad da suke girma. Idan kana fama da cutar da ake kira bipolar disorder ko kuma wani irin cutar bakin ciki, ka duba talifin nan “Ta Yaya Zan Daina Bakin Ciki?”