TAMBAYOYIN MATASA
Me Zan Yi Idan Na Taka Dokar Iyayena?
A kusan kowane iyali, akwai dokoki da iyaye suke bayarwa kamar su, lokacin da ya kamata yara su dawo gida, da yawan lokacin da ya kamata su yi suna amfani da na’urori, da kuma yadda za su rika daraja mutane.
Me za ka yi idan ka taka daya daga cikin dokokin da iyayenka suka kafa? Ba za ka iya canja abin da ya riga ya faru ba, amma akwai abin da za ka iya yi don kada yanayin ya kara muni. Za mu tattauna abubuwan nan a wannan talifin.
Abin da bai kamata ka yi ba
Idan iyayenka ba su san cewa ka taka wata doka ba, mai yiwuwa za ka yi kokarin boye laifinka.
Idan kuma sun san cewa ka taka dokarsu, mai yiwuwa za ka so ka ba da hujja ko kuma ka dora wa wani laifi.
Babu ko daya daga zabin nan da ya dace. Me ya sa? Domin idan ka boye laifin da ka yi ko ka ba da hujja, hakan zai nuna cewa ba ka manyanta ba. A maimakon haka, iyayenka za su ga cewa yaranta na damunka.
Wata mai suna Diana ta ce: “Yin karya ba zai magance matsalar ba. A kwana a tashi, iyayenka za su san gaskiyar abin da ya faru, kuma horon da za su yi maka zai fi wanda ya kamata su yi maka da a ce ka gaya musu gaskiya.”
Abin da ya kamata ka yi
Ka yarda cewa ka yi laifi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duk wanda ya rufe zunubansa, ba zai ci gaba ba.” (Karin Magana 28:13) Iyayenka sun san cewa kai ajizi ne. Amma suna so ka fadi gaskiya.
Wata mai suna Olivia ta ce: “Iyayenka za su iya gafarta maka idan ka gaya musu gaskiya. Idan kana gaya wa iyayenka gaskiya, za su yarda da kai.”
Ka nemi gafara. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukanku ku yi wa juna hidima cikin saukin kai.” (1 Bitrus 5:5) Saukin kai zai taimake ka ka nemi gafara ba tare da ka ba da hujja ba.
Wata mai suna Heather ta ce: “Idan mutum yana ba da hujja a kowane lokaci, a hankali a hankali zuciyarsa za ta daina damunsa idan ya yi laifi.”
Kar ka ki horo. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku ji horarwata.” (Karin Magana 8:33) Ka amince da duk horon da iyayenka suka yi maka ba tare da yin gunaguni ba.
Wani mai suna Jason ya ce: “Idan ka ci gaba da yin gunaguni, za ka dada bata wa iyayenka rai. Ka amince da horon da aka yi maka, kada ka yi ta tunanin yadda hakan zai takura maka.”
Ka yi kokari don iyayenka su sake yarda da kai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku yar da halin mutuntaka wanda kuke ciki a dā.” (Afisawa 4:22) Ka soma yin abubuwan da za su sa iyayenka su sake yarda da kai.
Wata mai suna Karen ta ce: “Idan ka soma yanke shawarwari masu kyau kuma ka nuna wa iyayenka cewa ba za ka maimaita kuskuren da ka yi ba, a hankali iyayenka za su amince da kai.”
SHAWARA: Ka yi fiye da abin da iyayenka suka ce ka yi don ka nuna musu cewa za su iya yarda da kai. Alal misali, idan ka je wani wuri, ka kira iyayenka tun kafin ka isa gida don ka gaya musu cewa kana hanya, ko da ba za ka isa gida latti ba. Hakan zai sa iyayenka su gane cewa kana so su sake yarda da kai.