Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Dole Ne In Zabi Irin Wakar da Zan Ji?

Dole Ne In Zabi Irin Wakar da Zan Ji?

 Carla ta ce: “Idan ina yin shiri domin ayyukana na yau da kullum, sai in kunna waka. Idan na soma tuki, ina saka waka. Idan ina shakatawa a gida ko ina shara ko ma ina karatu ne, a koyaushe ina sauraron waka.”

 Kai ma kana son waka kamar Carla? Idan e ce amsarka, to wannan talifin zai taimaka maka ka mori amfanin waka, ka guje wa hadarori da ke tattare da waka kuma ka zabi waka mai kyau.

 Amfanin waka

 Sauraron waka yana kama da cin abinci domin kana bukatar ka san irin wakar ta dace da kai da kuma yawan lokaci da ya kamata ka yi kana sauraronta. Ka yi la’akari da wannan:

  •   Waka za ta iya sa zuciyarka ta wartsake.

     Mark ya ce: “Idan ina bakin ciki kuma na saka wakar da na fi so, nan da nan sai in wartsake.”

  •   Waka za ta iya sa ka tuna baya.

     Sheila ta ce: “Sau da yawa, wani irin waka takan tuna mini da wani abin da ya taba faruwa, saboda haka a duk lokacin da na ji wannan wakar sai in yi farin ciki.”

  •   Waka tana iya kawo hadin kai.

     Tammy ta ce: “Akwai lokacin da na halarci wani taron kasashe da Shaidun Jehobah suka yi kuma sa’ad da ake waka ta karshe sai na soma kuka. Ko da yake yarenmu ba daya ba, sautin ya hada kanmu.”

  •   Waka za ta iya sa ka koyi halaye masu kyau.

     Anna ta ce: “Idan mutum yana koyan yin amfani da wani kayan kida, yana bukatar ya kame kansa kuma ya zama mai hakuri domin kida ba abin da mutum zai koya a cikin kwana daya ba ne. Sai ka yi amfani da kayan kidan sau da sau kafin ka kware.”

 Ka sani? Littafin da ya fi girma a cikin Littafi Mai Tsarki shi ne littafin Zabura kuma yana dauke da wakoki 150.

Ka rika zaban wakar da za ka saurara kamar yadda kake zaban abinci

 Hadarori

 Wasu wakokin suna kama da gurbataccen abinci da ke da hadari. Ga dalilan da suka sa muka fadi hakan.

  •   Wasu wakoki suna dauke da kalaman batsa.

     Hannah ta ce: “Kamar dai yawancin wakokin da suke tashe game da jima’i ne. Ba a ma boye hakan yanzu.”

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ma a ko ambaci fasikanci da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninku, domin kuwa bai dace da tsarkaka ba.” (Afisawa 5:3, Littafi Mai Tsarki) Za ka iya tambayar kanka, ‘Shin wakar da nake saurara tana hana ni bin wannan shawarar?’

  •   Wasu wakokin za su iya sa ka bakin ciki.

     Tammy ta ce: “A wasu lokuta nakan kwanta da dare ina sauraron wakar da ke sa ni yin tunani mai tsanani. Irin wannan wakar tana sa ni bakin ciki sosai.”

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka kiyaye zuciyarka gaba da dukan abin da ka ke kiyayewa.” (Misalai 4:23) Ka tambayi kanka, ‘Shin wakar da nake ji tana sa ni in yi tunanin banza ne?’

  •   Wasu wakokin za su iya sa ka fushi.

     John ya ce: “Sauraron wakar da kalaman suna nuna cewa mawakin yana fushi ko kuma ya tsane kansa yana da hadari a gare ni. Na lura cewa nakan yi fushi sosai bayan na saurari irin wannan wakar. Iyalina ma sun lura da hakan.”

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku kawar da dukan wadannan; fushi, hasala, keta, tsegumi, alfasha daga cikin bakinku.” (Kolosiyawa 3:8) Za ka iya tambayar kanka, ‘Wakar da nake sauraro takan sa ni fushi ko kuma kasancewa da halin ko-in-kula game da wasu?’

 Mene ne ya kamata ka yi? Ka rika zaban wakar da za ka saurara. Abin da wata matashiya mai suna Julie take yi ke nan. Ta ce: “A kullum ina bincika wakokin da nake saurara kuma ina share wadanda ba su da kyau. Ko da yake yin hakan bai da sauki, na san cewa abin da ya dace in rika yi ke nan.”

 Wata matashiya mai suna Tara ma tana kokarin yin hakan. Ta ce: “A wasu lokatai nakan ji wani sauti mai dadi a rediyo, amma bayan na saurari kalaman wakar sai in gane cewa ya kamata in canja tashar rediyon. Yin hakan yana nan kamar na dan gutsura rake mai zakin tsiya sai na yar da saura! Amma na san cewa idan na iya canja tashar da ake yin wakar banza a yanzu, hakan zai ba ni karfin guje wa yin jima’i kafin aure. Ba na son in dauka kamar wakar da nake saurara ba za ta iya shafan rayuwata ba.”