Allah Zai Gafarta Mini Kuwa?
Amsar Littafi Mai Tsarki
E, Allah zai gafarta maka idan ka dauki matakai da ya kamata. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah yana “hanzarin gafartawa” kuma yana ‘gafartawa a yalwace.’ (Nehemiya 9:17; Zabura 86:5; Ishaya 55:7) Idan ya gafarta mana, yana yin hakan gaba daya, wato yana “shafe” ko kuma kawar da zunubanmu. (Ayyukan Manzanni 3:19) Kari da haka, idan Allah ya gafarta mana ba ya sake tuhumarmu da laifin, domin ya ce: “Ba ni kuwa kara tuna da zunubinsu.” (Irmiya 31:34) Muddin ya gafarta mana, ba ya tuna da zunubanmu a kai a kai don ya yi mana horo.
Ba kasawa ba ne yake sa Allah ya gafarta mana. Kari ga haka, ba ya canja ka’idodinsa. Wannan dalilin ne ya sa ya ki ya gafarta ma wasu zunubansu.—Joshua 24:19, 20.
Matakai da ya kamata mutum ya dauka idan yana son Allah ya gafarta masa
Ka amince cewa zunubin da ka yi ya saba wa ka’idodin Allah. Mai yiwuwa abin da ka yi ya bata ma wasu rai, amma ya kamata ka san cewa ainihi dai, abin da ka yi zunubi ne a gaban Allah.—Zabura 51:1, 4; Ayyukan Manzanni 24:16.
Ka roki gafara daga wurin Allah.—Zabura 32:5; 1 Yohanna 1:9.
Ka yi bakin ciki sosai don zunubin da ka yi. Irin wannan “bacin zuciya” ko kuma bakin ciki yana sa mutum ya tuba. (2 Korintiyawa 7:10) Hakan ya kunshi yin da-na-sani a kan abubuwan da ka yi da suka sa ka yin zunubi.—Matta 5:27, 28.
Saboda haka, ka canja halinka, wato, ‘ka tuba.’ (Ayyukan Manzanni 3:19) Hakan yana iya nufin za ka guji maimaita zunubin da ka yi ko kuma ka canja salon rayuwarka da tunaninka.—Afisawa 4:23, 24.
Ka kokarta ka yi gyara. (Matta 5:23, 24; 2 Korintiyawa 7:11) Ka nemi gafara daga wurin wadanda zunubinka ya shafe su kuma ka yi iyakacin kokarinka ka biya diyya don duk wani abin da ka lalace.—Luka 19:7-10.
Ka roki Allah ya gafarta maka domin fansar Yesu. (Afisawa 1:7) Kafin a amsa addu’arka dole ne ka gafarta wa wadanda suka yi maka laifi.—Matta 6:14, 15.
Idan zunubin da ka yi yana da tsanani, ka gaya wa wani da zai iya taimaka maka ka kyautata dangantakarka da Allah kuma zai yi addu’a a madadinka.—Yakub 5:14-16.
Karyace-karyace a kan yadda Allah yake gafarta zunubi
“Zunubina ya yi yawa sosai saboda haka ba za a gafarta mini ba.”
Allah zai gafarta mana zunubanmu idan muka bi wadannan matakai da aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki, domin yana matukar son ya gafarta mana. Yana iya gafarta zunubai masu tsanani har da wadanda akan maimaita a wasu lokuta.—Misalai 24:16; Ishaya 1:18.
Alal misali, Allah ya gafarta wa Dauda, Sarkin Isra’ila bayan ya yi zina da kuma kisan kai. (2 Sama’ila 12:7-13) Ya kuma gafarta wa manzo Bulus wanda yake ganin kamar shi ne mai zunubi mafi girma a duniya. (1 Timotawus 1:15, 16) Har ma Yahudawa na karni na farko da suka kashe Yesu Almasihu, sun sami gafara sa’ad da suka tuba.—Ayyukan Manzanni 3:15, 19.
“Idan na gaya ma wani firist ko shugaban addini zunubin da na yi, zai gafarta mini.”
Idan mutum ya yi wa Allah zunubi, babu wani da yake da iko ya gafarta masa wannan zunubin, sai Allah. Idan muka gaya wa wani zunubin da muka yi, hakan zai iya taimaka mana mu daina yin zunubin. Amma Allah ne kadai yake da iko ya gafarta mana zunubanmu.—Afisawa 4:32; 1 Yohanna 1:7, 9.
Idan haka ne, mene ne Yesu yake nufi sa’ad da ya gaya wa manzanninsa cewa: “Duk wadanda kuka gafarta wa zunubansu, an gafarta musu ke nan. Duk wadanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta ba ke nan.” (Yohanna 20:23, Littafi Mai Tsarki) Yana magana ne game da ikon da za a ba manzanninsa sa’ad da suka karbi ruhu mai tsarki.—Yohanna 20:22.
Kamar yadda aka yi alkawarinsa, manzannin sun sami wannan ikon sa’ad da aka ba su ruhu mai tsarki a shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu. (Ayyukan Manzanni 2:1-4) Manzo Bitrus ya yi amfani da wannan ikon a lokacin da ya yanke wa Hananiya da Safiratu hukunci. Allah ya nuna wa Bitrus cewa karya suke yi, kuma hukuncin da Bitrus ya yanke ya nuna cewa ba za a taba gafarta musu ba.—Ayyukan Manzanni 5:1-11.
Irin wannan iko da aka samu ta wurin ruhu mai tsarki, har da baiwar yin warkarwa da kuma na yin magana a harsuna dabam-dabam sun shude bayan mutuwar manzannin. (1 Korintiyawa 13:8-10) Saboda haka, a yau babu wani dan Adam da yake da iko ya gafarta ma wani zunubin da ya yi.