Labarin Nuhu da Ambaliya, Tatsuniya Ce?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Ambaliyar ta faru da gaske. Allah ya sa a yi ambaliyar ne don ya hallaka mugaye, amma ya sa Nuhu ya gina jirgin ruwa don a ceci mutanen kirki da kuma dabbobi. (Farawa 6:11-20) Muna iya gaskata cewa ambaliyar ta faru da gaske domin Littafi Mai Tsarki da “hurarre” littafi ne daga Allah ya yi magana a kai.—2 Timoti 3:16.
Gaskiya ce ko tatsuniya?
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Nuhu mutum ne da ya rayu da gaske kuma Ambaliyar ta faru da gaske ba tatsuniya ko kuma labari ba ne.
Marubutan Littafi Mai Tsarki sun gaskata cewa Nuhu mutum ne da ya rayu da gaske. Alal misali, marubutan Littafi Mai Tsarki Ezra da Luka ’yan tarihi ne da suka kware kuma sun yi bincike sosai kafin suka ambata sunan Nuhu sa’ad da suke lissafta sunayen iyalan Isra’ila. (1 Tarihi 1:4; Luka 3:36) Marubutan Linjila Matiyu da Luka sun rubuta abin da Yesu ya ce game da Nuhu da kuma Ambaliya.—Matiyu 24:37-39; Luka 17:26, 27.
Ban da haka, annabi Ezekiyel da kuma manzo Bulus sun ambata Nuhu a matsayin mutumin da za a iya yin koyi da bangaskiyarsa da kuma adalcinsa. (Ezekiyel 14:14, 20; Ibraniyawa 11:7) Shin zai dace wadannan marubuta su ambata mutumin da bai taba rayuwa ba a matsayin wanda za a iya bin misalinsa? Hakika, Nuhu da kuma wasu maza da mata masu aminci sun kafa misali mai kyau da za mu iya bi domin sun rayu da gaske.—Ibraniyawa 12:1; Yaƙub 5:17.
Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da ambaliyar. Sa’ad da ake bayyana abin da ya faru a lokacin ambaliyar, ba a soma da furucin nan “ga ta nan ga ta nan ku” don a nuna cewa tatsuniya ce ba. A maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya ambata shekara da wata da kuma rana da abubuwan da suke da alaka da ambaliyar suka faru. (Farawa 7:11; 8:4, 13, 14) Kari ga haka, ya fadi yadda girman jirgin da Nuhu ya gina yake. (Farawa 6:15) Wannan karin bayanin ya nuna cewa da gaske ambaliyar ta faru ba tatsuniya ba ce.
Me ya sa aka yi ambaliyar?
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa kafin ambaliyar, “muguntar ’yan Adam ta yi yawa.” (Farawa 6:5) Ya kara da cewa a wajen Allah “duniya duka ta ɓaci” domin ana mugunta da kuma lalata sosai.—Farawa 6:11; Yahuda 6, 7.
Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa mugayen mala’iku ne suka jawo duka wadannan matsalolin domin sun bar sama kuma suka zo duniya suka yi lalata da ’yan Adam. Wadannan mala’ikun sun haifi ’ya’ya da ake kira Nephilim da suka jawo wa mutane wahala sosai. (Farawa 6:1, 2, 4) Allah ya dau matakin tsabtace duniya daga mugunta domin mutane masu adalci su sake soma rayuwa.—Farawa 6:6, 7, 17.
Mutane sun san cewa za a yi ambaliyar?
Kwarai kuwa. Allah ya gaya wa Nuhu abin da zai faru kuma ya umurce shi ya gina jirgi don ya ceci iyalinsa da kuma dabbobi. (Farawa 6:13, 14; 7:1-4) Nuhu ya yi wa mutane wa’azi game da ambaliyar da za a yi, amma ba su saurare shi ba. (2 Bitrus 2:5) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kafin su san abin da ake ciki, babbar ambaliyar ta zo ta kwashe su duka.”—Matiyu 24:37-39.
Yaya kamanin jirgin Nuhu yake?
Jirgin yana da girma kuma yana nan ne kamar akwati, tsawonsa wajen kafa 437 fadinsa ya kai kafa 73 tsayinsa kuma ya kai kafa 44. Nuhu ya gina jirgi ne da itace mai kyau kuma ya shafe shi da mān kwalta ciki da waje. Jirgin yana da hawa uku da kuma dakuna a ciki. Akwai kofa da kuma wundo a sama. Watakila rufin jirgin yana da tsayi don kada ruwa ya rika kwanciya a saman rufin.—Farawa 6:14-16.
Shekaru nawa ne Nuhu ya yi yana gina jirgin?
Littafi Mai Tsarki bai fadi adadin shekaru da Nuhu ya yi yana gina jirgin ba, amma kamar ya dau shekaru da yawa yana yin hakan. Nuhu ya fi shekaru 500 sa’ad da aka haifi dansa na fari, kuma yana dan shekara 600 sa’ad da aka yi ambaliyar. a—Farawa 5:32; 7:6.
Allah ya umurci Nuhu ya gina jirgin bayan yaransa uku sun yi girma, sun yi aure, kuma hakan watakila ya dauki wajen shekaru 50 ko 60. (Farawa 6:14, 18) Idan hakan gaskiya ne, za mu iya cewa Nuhu ya dauki wajen shekaru 40 ko 50 yana gina jirgin.
a Don karin bayani game da tsawon rayuwar mutane kamar Nuhu, ka duba talifin nan “Did People in Bible Times Really Live So Long?” a Hasumiyar Tsaro na 1 ga Disamba, 2010.