Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Azumi?
Amsar Littafi Mai Tsarki
A zamanin dā, Allah yana amincewa da azumi da aka yi da manufa mai kyau. Amma idan don munafurci aka yi, hakan yana sa Allah ya ki nuna wa mutumin alheri. Littafi Mai Tsarki bai hana mutane a yau yin azumi ba.
A wane irin yanayi ne wasu a Littafi Mai Tsarki suka yi azumi?
A lokacin da suke neman taimako ko shawara daga wurin Allah. Mutanen da suka yi doguwar tafiya zuwa Urushalima sun yi azumi ne domin su nuna cewa suna bukatar taimakon Allah da gaske. (Ezra 8:21-23) A wasu lokuta Bulus da Barnaba sun yi azumi kafin su nada dattawa a ikilisiya.—Ayyukan Manzanni 14:23
Sa’ad da ake mai da hankali ga nufin Allah. Bayan da aka yi masa baftisma, Yesu ya yi azumi na kwanaki 40 kafin ya fara wa’azi. Ya yi hakan ne domin ya shirya kansa don yin nufin Allah.—Luka 4:1, 2
Sa’ad da mutum ya tuba don laifofinsa. Allah ya gaya wa Isra’ilawa, ta wurin annabi Joel: “Amma ku yanzu, in ji Ubangiji, ku juyo mani da dukan zuciyarku, tare da azumi da kuka da bakin ciki.”—Joel 2:12-15
Sa’ad da ake bikin Ranar Kafara. A dokar da Allah ya ba wa al’ummar Isra’ila ya umurce su su rika yin azumi a Ranar Kafara da suke yi kowace shekara. a (Levitikus 16:29-31) Ya dace a yi azumi a wannan lokacin saboda yana tuna wa Isra’ilawa cewa su ajizai ne kuma suna bukatar Allah ya gafarta masu.
Wadanne ra’ayoyi ne da ba su dace ba ke sa mutane yin azumi?
Don a burge mutane. Yesu ya ce yin azumi ba abin da wasu za su sani ba ne amma ya kamata ya zama tsakanin mutumin da Allah.—Matta 6:16-18.
Don ka nuna kai mai adalci ne. Yin azumi ba ya sa mutum ya zama mai halin kirki ko kuma ya sa mutum ya kasance da dangantaka mai kyau da Allah.—Luka 18:9-14
Don mutum yana so Allah ya yafe masa zunubin da ya yi da gangan. (Ishaya 58:3, 4) Mutanen da ke masa biyayya kuma sun tuba da zuciya daya ne Allah yake amincewa da azuminsu.
Yin azumi don mutumin yana bin wani addini. (Ishaya 58:5-7) A wannan fannin, Allah yana kama da uba wanda ’ya’yansa suke masa biyayya domin wata farilla kawai, ba daga zuciyarsu ba.
Shin an bukaci Kiristoci su rika yin azumi ne?
A’a. Allah ya bukaci Isra’ilawa su yi azumi a Ranar Kafara, amma ya sa an daina yin hakan bayan Yesu ya fanshi mutanen da suka tuba. (Ibraniyawa 9:24-26; 1 Bitrus 3:18) Kiristoci ba sa bin dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa, wanda Ranar Kafara ke cikin. (Romawa 10:4; Kolossiyawa 2:13, 14) Saboda haka, kowanne Kirista ne zai yanka shawarar yin azumi ko a’a.—Romawa 14:1-4.
Kiristoci sun san cewa azumi bai shafi ibadarsu ba. Littafi Mai Tsarki bai ce azumi zai iya sa mutum farin ciki ba. A maimakon haka, bauta wa Jehobah ne ke sa mutum farin ciki, domin Jehobah Allah ne mai farin ciki.—1 Timotawus 1:11; Mai-Wa’azi 3:12, 13; Galatiyawa 5:22
Ra’ayin da bai dace ba game da azumi
Ra’ayi: Manzo Bulus ya ce wa ma’aurata Kiristoci su rika yin azumi.—1 Korintiyawa 7:5.
Gaskiyar: Rubuce-rubuce na farko na littafin 1 Korintiyawa 7:5 ba su ambaci azumi ba. b Don haka, masu kofan Littafi Mai Tsarki ne suka kara kalmar nan azumi, ba a wannan ayar kadai ba amma har da littafin Matta 17:21 da Markus 9:29 da kuma Ayyukan Manzanni 10:30. An cire wannan kalmar a yawancin juyin Littafi Mai Tsarki domin tun asali ba ta ciki.
Ra’ayin da bai dace ba: Ya kamata Kiristoci su rika yin azumi domin suna tunawa da yadda Yesu azumin kwanaki 40 a jeji bayan an yi masa baftisma.
Gaskiyar: Yesu bai ba da umurni cewa Kiristoci su rika azumi ba, kuma babu wasu Nassosin da suka nuna cewa Kiristoci a dā sun yi hakan. c
Ra’ayin da bai dace ba: Ya kamata Kiristoci su rika azumi a lokacin tunawa da mutuwar Yesu.
Gaskiyar: Yesu bai umurci almajiransa su rika yin azumi a lokacin tunawa da mutuwarsa ba. (Luka 22:14-18) Ko da yake Yesu ya ce almajiransa za su yi azumi lokacin mutuwarsa, ba umurni ya ba su ba amma yana fadan abin da zai faru ne a lokacin. (Matta 9:15) Littafi Mai Tsarki ya umurce Kiristoci su ci abinci a gida kafin su halarci taron Tunawa da Mutuwar Yesu.—1 Korintiyawa 11:33, 34.
a Allah ya gaya wa Isra’ilawa cewa: “Za ku wahalar da rayukanku” a Ranar Kafara. (Levitikus 16:29, 31) Hakan yana nufin yin azumi. (Ishaya 58:3) Saboda haka, juyin Contemporary English Version ya yi amfani da furucin nan: “Za ku zauna ba cin abinci don ku nuna bakin ciki saboda laifuffukanku.”
b Ka duba littafin nan A Textual Commentary on the Greek New Testament, by Bruce M. Metzger, bugu na uku, shafi na 554.
c Game da tarihin kwanaki 40 na azumin Lent, littafin nan New Catholic Encyclopedia ya ce: “A karnuka uku na farko, lokacin azumi saboda bikin paschal [Easter] ba ya ma shige sati daya; a kan yi shi ne a rana daya ko biyu kawai. . . Ambata kwanaki 40 na azumi ya auku ne a taron Majalisar Nicaea (325), ko da yake dai wasu masana ba su yarda cewa yana nufin Lent ba.”