Me Zai Taimaka Mana Mu Kasance da Halin Sa Zuciya ko Bege?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Littafi Mai Tsarki ya ce Allah yana so ya ba mu “sa zuciya da rayuwa ta nan gaba.” a (Irmiya 29:11) Wani dalilin da ya sa Allah ya ba mu Littafi Mai Tsarki shi ne “mu zama da sa zuciya ta wurin . . . karfafawa wadanda Rubutacciyar Maganar Allah sukan ba mu.” (Romawa 15:4) Kamar yadda za mu gani, shawara da ke cikin Littafi Mai Tsarki za ta taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace game da matsalolinmu na yau da kullum. Kuma alkawarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki zai sa mu kasance da bege.
A shafin nan za ka ga
Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai sa mu kasance da raꞌayin da ya dace?
Ta wajen gaya mana abubuwan da za mu iya yi don mu inganta rayuwarmu, Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace. Ga wasu misalai.
Ka nemi shawara daga Littafi Mai Tsarki. Zabura 119:105 ta ce: “Maganarka fitila ce ga kafafuna, haske kuma ga hanyata.” Ana iya yin abubuwa biyu da wuta mai haske sosai. Za ta iya haskaka abin da ke gabanmu da kuma abin da ke da nisa. Hakazalika, shawarwarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu san yadda za mu bi da matsalolin da muke fuskanta a yanzu. Kuma zai sa mu kasance da raꞌayin da ya dace yau da kullum. Koyarwa da ke cikin Littafi Mai Tsarki zai karfafa mu kuma ya ‘farantar da zuciyarmu.’ (Zabura 19:7, 8) Ban da haka ma, Littafi Mai Tsarki ya ba da karin haske game da nufin Allah don duniya da kuma ꞌyan Adam. Wannan begen zai sa mu rika farin ciki kuma mu kasance da gamsuwa.
Ka bar mutane su taimaka maka. Idan muna cikin wani yanayi mai wuya, za mu iya ganin kamar zai fi mu guji ꞌyanꞌuwanmu ko kuma abokai. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa bai kamata mu yi hakan ba, don zai sa mu dauki matakan da ba su dace ba. (Karin Magana 18:1) ꞌYanꞌuwa da abokanka za su taimaka maka ka yi tunanin kirki. Za su iya ba ka shawarwari game da yadda za ka magance wani mawuyacin yanayi. (Karin Magana 11:14) Kari ga haka, za su iya karfafa mu don mu iya jimre yanayi da muke ciki har lokacin da abubuwa za su canja.—Karin Magana 12:25.
Ka yi adduꞌa ga Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Danka wa Yahweh damuwarka, shi kuwa zai lura da kai, ko kadan ba zai bar masu adalci su jijjigu ba.” b (Zabura 55:22) Shi ya sa ake kiran Jehobah “Allah mai kawo sa zuciya.” (Romawa 15:13) Za ka iya gaya masa ‘dukan damuwarka,’ da tabbaci cewa zai taimaka maka. (1 Bitrus 5:7) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zai mai da ku cikakku, zai kafa ku, zai kuma karfafa ku.”—1 Bitrus 5:10.
Ka bar matsaloli su karfafa begenka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wadanda suka saurare [Allah] za su zauna lafiya. Za su kuwa zauna rai a kwance, babu tsoron azaba.” (Karin Magana 1:33) Saꞌad da mahaukaciyar guguwa ta lalace gidan wata mata mai suna Margaret a Ostiraliya, ta yi hasara dukiyoyinta da yawa. Maimakon ta rika bakin ciki, ta koyi darasi cewa mutum zai iya yin hasara dukiyarsa dare daya. Bayan abin da ya faru da ita, ta kuduri niyya cewa za ta mai da hankali ga abubuwan da suka fi muhimmanci. Abubuwan su ne, iyalinta da abokanta da dangantakarta da Allah da kuma alkawuran da ke Littafi Mai Tsarki.—Zabura 37:34; Yakub 4:8.
Mene ne Littafi Mai Tsarki ya yi wa dukan ꞌyan Adam Alkawarinsa?
Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa ꞌyan Adam za su yi farin ciki a nan gaba kuma duniya za ta zama aljanna. Kuma hakan zai faru nan ba da dadewa ba. Matsalolin da ꞌyan Adam suke fuskanta a yau sun nuna cewa muna “kwanakin karshe” na zamanin nan. (2 Timoti 3:1-5) Nan ba da dadewa ba, Allah zai dauki mataki kuma ya kawar da rashin adalci da kuma shan wahala. Zai yi amfani da Mulkinsa don ya cim ma wadannan abubuwan. (Daniyel 2:44; Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 11:15) Yesu yana maganar gwamnatin nan saꞌad da ya yi adduꞌa cewa: “Mulkinka ya zo, bari a yi nufinka a cikin duniya.”—Matiyu 6:9, 10.
An fadi nufin Allah dalla-dalla a cikin Littafi Mai Tsarki. Ga wasu matsalolin da Mulkin Allah zai kawar:
Ba za a kara yunwa ba. “Kasa ta ba da amfaninta.”—Zabura 67:6.
Ba za a kara cututtuka ba. “Ba mazaunin kasar da zai ce, ‘Ina ciwo.’ ”—Ishaya 33:24.
Ba za a kara mutuwa ba. Allah “zai share musu dukan hawaye daga idanun [ꞌyan Adam]. Babu sauran mutuwa, ko bakin ciki, ko kuka, ko azaba. Gama abubuwan dā sun bace.”—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:3, 4.