Wane ne Magabcin Kristi?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Magabcin Kristi ba mutum ɗaya kawai ko kuma wani rukuni ba ne, domin Littafi Mai Tsarki ya ce da akwai “magabtan Kristi da yawa.” (1 Yohanna 2:18) Maimakon haka, furucin nan “magabcin Kristi,” da aka ɗauko daga kalmar Helenanci yana nufin “yin gāba (ko kuma a maimakon) Kristi.” Ƙari ga haka, yana nuni ga wanda yake yin waɗannan abubuwa:
Ya ƙi cewa Yesu ne Kristi (Almasihu) ko kuma bai yarda cewa shi Ɗan Allah ne.—1 Yohanna 2:22.
Yana gāba da Kristi, Shafaffe na Allah.—Zabura 2:1, 2; Luka 11:23.
Yana yin abubuwa kamar shi ne Kristi.—Matta 24:24.
Yana tsananta wa mabiyan Kristi, tun da yake Yesu ya ɗauka cewa shi ne ake tsananta wa idan aka tsananta wa mabiyansa.—Ayyukan Manzanni 9:5.
Yana da’awa cewa shi Kirista ne yayin da yake ayyukan mugunta ko kuma ruɗin mutane.—Matta 7:22, 23; 2 Korintiyawa 11:13.
Ban da mutane ɗaɗɗaya da suka yin irin waɗannan ayyukan da ake ce su magabtan Kristi ne, Littafi Mai Tsarki ya kuma ambata su a matsayin rukuni, wato “magabcin Kristi.” (2 Yohanna 7) Magabcin Kristi ya fara bayyana ne a zamanin manzanni kuma ya wanzu har zuwa yau. A cikin Littafi Mai Tsarki an annabta cewa hakan zai faru.—1 Yohanna 4:3.
Yadda za a gane magabtan Kristi
Suna ɗaukaka ra’ayin ƙarya game da Yesu. (Matta 24:9, 11) Alal misali, waɗanda suke koyar da Allah-Uku-Cikin-Ɗaya ko kuma Yesu ne Allah Maɗaukaki, suna ƙin koyarwar Yesu, wanda ya ce: “Uba ya fi ni girma.”—Yohanna 14:28.
Magabtan Kristi suna ƙin abin da Yesu ya ce game da yadda Mulkin Allah yake sarauta. Alal misali, wasu shugabanan addinai sun ce Kristi yana yin ayyuka ta wurin gwamnatocin ’yan Adam.
Amma, wannan koyarwa ta saɓa wa abin da Yesu ya ce: “Mulkina ba na wannan duniya ba.”—Yohanna 18:36.
Sun ce Yesu ne Ubangijinsu, amma ba sa bin umurninsa, wanda ya ƙunshi yin wa’azin bishara game da Mulkin.—Matta 28:19, 20; Luka 6:46; Ayyukan Manzanni 10:42.