Me Ya Sa Yesu Ya Mutu?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Yesu ya mutu don Allah ya gafarta wa ’yan Adam zunubansu kuma ya ba su damar rayuwa har abada. (Romawa 6:23; Afisawa 1:7) Kari ga haka, mutuwar Yesu ta tabbatar mana cewa ‘yan Adam za su iya kasancewa da aminci ga Allah ko da ana jarraba su.—Ibraniyawa 4:15.
Bari mu tattauna yadda mutuwar mutum daya zai iya cim ma abubuwa da yawa haka.
Yesu ya mutu don “gafarar zunubanmu.”—Kolosiyawa 1:14.
Allah ya halicci mutum na fari, wato, Adamu a matsayin kamiltaccen mutum. Amma daga baya ya yi wa Allah rashin biyayya. Kuma hakan ya sa dukan ‘yan Adam sun zama masu zunubi. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Masu dumbun yawa sun zama masu zunubi ta rashin biyayyar mutum daya.’—Romawa 5:19, Littafi Mai Tsarki.
Yesu kamili ne kuma bai taba yin zunubi ba. Hakan ya sa shi ne ya cancanci ya zama “hadayar sulhu saboda gafarta zunubanmu.” (1 Yohanna 2:2, LMT) Rashin biyayyar Adamu ya jefa ’yan Adam cikin zunubi, amma mutuwar Yesu tana wanke zunuban dukan wadanda suka ba da gaskiya a gare shi.
Za mu iya cewa Adamu ya sayar da mu ga zunubi. Amma Yesu ya mutu domin ya fanshe mu daga zunubi. Saboda haka, idan mun “yi zunubi, muna da mai taimako wurin Uba, Yesu Kristi mai adalci.”—1 Yohanna 2:1.
Yesu ya mutu ‘domin dukan wanda ya ba da gaskiya gare shi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.’—Yohanna 3:16.
Ko da yake Allah ya halicci Adamu don ya rayu har abada, zunubinsa ya jawo masa mutuwa. Ta wurin Adamu, “zunubi ya shigo cikin duniya . . . , mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.”—Romawa 5:12.
Akasin abin da Adamu ya jawo, mutuwar Yesu ta wanke zunuban ’yan Adam kuma tana ba duk wanda ya ba da gaskiya gare shi damar yin rayuwa har abada. Ga yadda Littafi Mai Tsarki ya takaita wannan batun, ya ce: “Kamar yadda zunubi ya ja-goranci [mutane] zuwa mutuwa, haka nan kuma alheri zai kai ga adalci zuwa rai na har abada ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu.”—Romawa 5:21.
Hakika, har wa yau mutane suna mutuwa bayan sun yi wasu shekaru. Amma Allah ya yi alkawari cewa zai ba masu adalci rai na har abada kuma ko da sun mutu, zai ta da su daga mutuwa domin su amfana daga mutuwar Yesu.—Zabura 37:29; 1 Korintiyawa 15:22.
Yesu ‘ya yi biyayya har mutuwa,’ kuma hakan ya nuna cewa ’yan Adam za su iya rike amincinsu ga Allah ko da ana jarraba su.—Filibiyawa 2:8.
Duk da cewa Adamu kamiltacce ne, ya yi wa Allah rashin biyayya don ya yi kwadayin abin da ba na shi ba. (Farawa 2:16, 17; 3:6) Daga baya, babban magabcin Allah, wato Shaidan, ya gaya wa Allah cewa babu dan Adam da zai yi wa Allah biyayya da zuciya daya, musamman ma idan hakan zai jefa rayuwarsa a cikin hadari. (Ayuba 2:4) Duk da abin da Shaidan ya fada, Yesu ya yi wa Allah biyayya kuma ya rike amincinsa ga Allah har ma a lokacin da za a kashe shi. (Ibraniyawa 7:26) Abin da Yesu ya yi ya tabbatar mana cewa: Dan Adam zai iya rike amincinsa ko da yana fuskantar jarrabobi.
Tambayoyi game da mutuwar Yesu
Me ya sa sai da Yesu ya sha wahala kuma ya mutu kafin ya fanshi ’yan Adam? Me ya sa Allah bai yafe zunubin kawai ba?
Dokar Allah ta ce, “hakkin zunubi mutuwa ne.” (Romawa 6:23) Tun kafin Adamu ya yi zunubi, Allah ya gaya masa cewa idan ya yi rashin biyayya zai mutu. (Farawa 3:3) Bayan da Adamu ya yi zunubi, abin da Allah ya gaya masa ya faru hakan, domin Allah “ba ya iya yin karya.” (Titus 1:2) Adamu ya sa ‘ya’yansa sun gāji zunubi daga wurinsa, har da mutuwa.
Da yake mu ajizai ne, mun cancanci mu mutu, amma Allah ya nuna mana yalwar “alherinsa.” (Afisawa 1:7) Yadda ya ba da dansa ya zo ya mutu don ya fanshe mu ya nuna cewa shi mai adalci ne da kuma jin kai.
Yaushe ne Yesu ya mutu?
Yesu ya mutu da “karfe uku na yamma” a ranar da Yahudawa suke Idin Ketarewa. (Markus 15:33-37, LMT) Kuma ranar ta yi daidai da ranar Jumma’a, 1 ga Afrilu 33, bayan haihuwar Yesu, bisa ga kwanan wata na zamaninmu.
A ina ne aka kashe Yesu?
An rataye Yesu a “wurin da ake ce da shi Wurin Kokon kai,” ko kuma wurin da ake “ce da shi da Yahudanci Golgotha.” (Yohanna 19:17, 18) A zamanin Yesu, wannan wurin yana ‘bayan kofar birnin’ Urushalima ne. (Ibraniyawa 13:12) Watakila yana kan tudu ne don Littafi Mai Tsarki ya ce wasu sun tsaya suna kallon yadda ake rataye Yesu “daga nesa.” (Markus 15:40) Amma yau, ba a san ainihin inda Golgotha yake ba.
A kan giciye ne aka kashe Yesu?
Ko da yake mutane da yawa sun dauka cewa an giciye Yesu ne, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yesu “da kansa fa ya dauki zunubanmu ya kai su cikin jiki nasa bisa itacen.” (1 Bitrus 2:24) Kalmomi biyu ne marubutan Littafi Mai Tsarki a Helenanci suka yi amfani da su sa’ad da suke kiran abin da aka kashe Yesu a kai, kuma kalmomin nan su ne stau·rosʹ da xyʹlon. Masana da yawa sun ce wadannan kalmomin suna nufin gungume ne.
Yaya ne ya kamata mu tuna da mutuwar Yesu?
A daren ranar da Yahudawa suke yin Idin Ketarewa, Yesu ya nuna wa mabiyansa yadda ya kamata su tuna mutuwarsa kuma ya ce musu, “Ku rika yin haka domin tunawa da ni.” (1 Korintiyawa 11:24) Awoyi bayan haka, sai aka kashe Yesu.
Marubutan Littafi Mai Tsarki sun kwatanta Yesu da dan ragon da ake hadaya da shi a Idin Ketarewa. (1 Korintiyawa 5:7) Kamar yadda Idin Ketarewa yake tuna wa Isra’ilawa yadda Allah ya cece su daga bauta a Masar, haka ma tunawa da mutuwar Yesu yana sa Kiristoci su tuna cewa an cece su daga zunubi da mutuwa. Ana yin Idin Ketarewa ne a kowace shekara a ranar 14 ga Nisan bisa ga kwanan watan Yahudawa, kuma Kiristoci na farko sukan taru a kowace shekara sau daya don su tuna da mutuwar Yesu.
Kowace shekara, miliyoyin mutane a fadin duniya suna taruwa a duk ranar da ta yi daidai da 14 ga Nisan, don su tuna da mutuwar Yesu.