Su Waye Ne Nephilim?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Nephilim mutane ne masu karfi sosai, da suke aikata mugunta. Su ’ya’yan mala’iku ne da suka yi wa Allah tawaye a sama sa’an nan suka yi lalata da ‘yan mata a zamanin Nuhu. a
Littafi Mai Tsarki ya ce “sai ’ya’yan Allah suka ga ‘yan mata na mutane kyawawa ne.” (Farawa 6:2) Wadannan “’ya’yan Allah” mala’iku ne da suka yi wa Allah tawaye sai suka “rabu da nasu wurin zama” a sama, suka canja jikinsu zuwa na mutane, kuma suka soma “dauko wa kansu mata dukan wadanda suka zaba.”—Yahuda 6; Farawa 6:2.
’Ya’yan da suka haifa sun zama mutane masu karfin gaske. (Farawa 6:4) Nephilim suna da karfi sosai kuma suna cin zalin mutane, har sun sa ana ta mugunta a duniya. (Farawa 6:13) Littafi Mai Tsarki ya kwatanta su da “karfafan mutane wadanda ke na dā, mutane masu suna.” (Farawa 6:4) Labarinsu na ban tsoro ne da kuma cin zali.— Farawa 6:5; Littafin Lissafi 13:33. b
Ra’ayoyin da ba su dace ba game da Nephilim
Karya: Nephilim suna da rai har yanzu a duniya.
Gaskiya: Jehobah ya hallaka duniya da ke cike da mugunta a zamanin Nuhu. An hallaka Nephilim tare da sauran mugayen mutane. Amma, Nuhu da iyalinsa ne kawai suka tsira don sune kadai a wannan lokacin suka yi wa Jehobah biyayya.—Farawa 6:9; 7:12, 13, 23; 2 Bitrus 2:5.
Karya: Mutane ne ubannin Nephilim.
Gaskiya: Ana kiran ubanninsu, “’ya’yan Allah.” (Farawa 6:2) Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar ne wajen kiran mala’iku. (Ayuba 1:6; 2:1; 38:7) Mala’iku suna da ikon su canja jikinsu zuwa na mutane. (Farawa 19:1-5; Joshua 5:13-15) Manzu Bitrus ya yi magana game da ‘ruhohin da suke cikin kurkuku, . . . wadanda a dā ba su yi biyayya ga Allah ba, ko da yake Allah ya yi hakuri da su a lokacin Nuhu.’ (1 Bitrus 3:19, 20, Juyi Mai Fitar da Ma’ana) Sa’ad da Yahuda marubucin Littafi Mai Tsarki yake magana game da batun, ya ce wasu mala’iku “ba su rike matsayi nasu ba, amma suka rabu da nasu wurin zama.”—Yahuda 6.
Karya: Nephilim mala’iku ne da suka sauko daga sama.
Gaskiya: Abin da aka rubuta a Farawa 6:4 ya nuna cewa Nephilim ba mala’iku ba ne, amma an haife su ne sakamakon lalata da mala’iku suka yi da ‘yan mata a duniya. Bayan da mala’ikun “suka dauko wa kansu mata dukan wadanda suka zaba,” sai Jehobah ya ce nan da shekaru 120 zai hallaka mugaye. (Farawa 6:1-3) Labarin ya dada da cewa, a “wadancan kwanaki,” sai mala’ikun da suka canja jikinsu suka “shiga wurin ’yan mata na mutane” wato, sun yi lalata da su kuma suka haife “karfafan mutane wadanda ke na dā,” wato Nephilim.—Farawa 6:4.
a Kalmar Ibrananci da aka fasara zuwa “Nephilim” watakila tana nufin “Masu Ka da Mutane.” Littafin nan Wilson’s Old Testament Word Studies ya ce kalmar tana nufin wadanda suke “fadiwa a kan mutane, suna kwace kayansu kuma su sa su fadi.”
b Babu shakka Isra’ilawa ‘yan leken asiri da aka ambata a Littafin Lissafi 13:33 sun ga mutanen da girmansu ya sa sun tuna da Nephilim da suka rasu karnuka da dama da suka shige.—Littafin Lissafi 13:33; Farawa 7:21-23.