Ta Yaya Za Ka San Allah da Kyau?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Za ka iya sanin Allah da kyau idan kana yin nazari game da shi, kuma kana yin abubuwan da za su faranta masa rai. Hakan zai sa Allah ya ‘yi kusa da kai.’ (Yakub 4:8) Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa “bai yi nesa da kowannenmu ba.”—Ayyukan Manzanni 17:27.
Abubuwan da za su taimaka mana mu san Allah
Karatun Littafi Mai Tsarki
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duk Rubutacciyar Maganar Allah hurarre ce daga wurinsa.”—2 Timoti 3:16.
Abin da hakan yake nufi: Allah ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki. Shi ne ya gaya wa marubutan Littafi Mai Tsarki abin da za su rubuta. Ta wajen Littafi Mai Tsarki ne Allah ya gaya mana irin rayuwar da yake so mu yi. Ya kuma gaya mana irin halayen da yake da su, kamar kauna da adalci da kuma jin kai.—Fitowa 34:6; Maimaitawar Shari’a 32:4.
Abin da za ka iya yi: Ka karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana. (Yoshuwa 1:8) Ka yi tunani a kan abin da ka karanta kuma ka tambayi kanka cewa: ‘Me wannan wurin yake koya min game da Allah?’—Zabura 77:12.
Alal misali, ka karanta Irmiya 29:11, sa’an nan ka tambayi kanka cewa: ‘Wane abu Allah yake shirya min? Alheri ko masifa? Shi Allah mai rama duk abin da aka yi masa ne ko yana so in yi rayuwa mai inganci a nan gaba?’
Ka yi la’akari da halittunsa
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Halin Allah ba abin da ake iya gani da ido ba ne. Amma tun halittar duniya an bayyana wadannan abubuwan a fili, ana kuma iya gane su bisa ga abubuwan da aka halitta.’—Romawa 1:20.
Abin da hakan yake nufi: Zane-zane sukan bayyana mana wani abu game da wanda ya yi zanen, kuma wata na’ura mai ban mamaki za ta iya bayyana mana wani abu game da wanda ya kirkiro ta. Haka ma, abubuwan da Allah ya halitta da muke gani za su iya nuna mana wasu halayen Allah. Alal misali, yadda kwakwalwarmu take aiki da kuma yadda Allah ya tsara ta ya nuna cewa Allah mai hikima ne. Kuma yadda Allah yake daidaita zafin rana da sauran taurari ya nuna irin ikon da Allah yake da shi.—Zabura 104:24; Ishaya 40:26.
Abin da za ka iya yi: Ka rika kallon abubuwan da Allah ya halitta da kyau kuma ka yi nazari a kansu. Yayin da kake hakan, ka tambayi kanka cewa, ‘Mene ne wannan halittar take koya min game da Allah?’ a Amma akwai abubuwa da yawa da halittun Allah ba za su iya koya mana game da Mahaliccinmu ba. Shi ya sa ya ba mu Littafi Mai Tsarki.
Ka kira Allah da sunansa
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zan kiyaye shi saboda ya san sunana. Zai kira gare ni, zan kuwa amsa masa.”—Zabura 91:14, 15.
Abin da hakan yake nufi: Allah, mai suna Jehobah ko kuma Yahweh, ya damu da wadanda suka san sunan shi kuma suna daraja sunan. b (Zabura 83:18; Malakai 3:16) Da yake Allah ya gaya mana sunansa, yana so mu san ko shi waye ne. Ya ce: “Ni ne Yahweh, sunana ke nan.”—Ishaya 42:8.
Abin da za ka iya yi: Ka rika kiran Allah da sunansa sa’ad da kake magana game da shi.
Ka yi magana da Jehobah ta wajen yin addu’a
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yahweh yana kurkusa ga masu kira gare shi.”—Zabura 145:18.
Abin da hakan yake nufi: Jehobah yana kusantar wadanda suke ba da gaskiya gare shi ta wajen yin addu’a. Addu’a, wani bangaren ibadarmu ga Allah ne kuma tana nuna cewa muna daraja shi sosai.
Abin da za ka iya yi: Ka rika yin addu’a a koyaushe. (1 Tasalonikawa 5:17) Ka gaya masa abin da ke damunka da yadda kake ji.—Zabura 62:8. c
Ka sa bangaskiyarka ta dada karfi
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “In ba tare da bangaskiya ba, ba ya yiwuwa a faranta wa Allah rai.”—Ibraniyawa 11:6.
Abin da hakan yake nufi: Idan muna so mu kusace Allah, dole ne mu kasance da bangaskiya. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ba yarda cewa akwai Allah ne kawai zai mu kasance da bangaskiya ba. Dole ne mu dogara gare shi da dukan zuciyarmu, mu kuma gaskata alkawuransa, sa’an nan mu yarda cewa ka’idodinsa sun fi na ’yan Adam. Kafin ka zama aminin wani, dole ka yarda da shi.
Abin da za ka iya yi: Sanin abin da ke Littafi Mai Tsarki ne zai sa mu kasance da bangaskiya. (Romawa 10:17) Don haka, ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ka gaya wa kanka cewa za ka iya dogara ga Allah da kuma ka’idodinsa. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin yin nazari da kai. d
Ka yi abin da ke faranta wa Allah rai
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kaunarmu ga Allah ita ce, mu kiyaye umarnansa.”—1 Yohanna 5:3.
Abin da hakan yake nufi: Za mu zama aminan Allah idan muna kaunarsa kuma muna iya kokarinmu mu yi masa biyayya.
Abin da za ka iya yi: Yayin da kake nazarin Littafi Mai Tsarki, ka lura da abin da Allah yake so da wanda ba ya so. Ka tambayi kanka cewa, ‘Me da me zan gyara a rayuwata don in faranta ran Mahaliccina?’—1 Tasalonikawa 4:1.
Idan ka bi ka’idodin Allah, zai kula da kai
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku dandana ku ga [cewa] Yahweh mai alheri ne”—Zabura 34:8.
Abin da hakan yake nufi: Allah yana so ka gani da kanka cewa shi mai alheri ne. Idan ka ga yadda yake taimaka maka kuma yake nuna maka kauna, za ka so ka kusace shi.
Abin da za ka iya yi: Yayin da kake karanta Littafi Mai Tsarki, ka rika bin abin da ka gani a ciki. Hakan zai sa ka amfana. (Ishaya 48:17, 18) Kari ga haka, ka lura da yadda rayuwar masu bin ka’idodin Allah take, yadda Allah yake taimaka musu su magance matsalolinsu, su inganta rayuwarsu da na iyalinsu, kuma su yi farin ciki. e
Karairayin da ake yi game da Allah
Karya: Allah yana da iko da kuma matsayi sosai, don haka, ba ya so mu yi kusa da shi.
Gaskiyar batun: Ko da yake Allah ne mafi iko da kuma matsayi, yana so mu kusace shi. A cikin Littafi Mai Tsarki akwai mata da maza da yawa da suka zama aminan Allah.—Ayyukan Manzanni 13:22; Yakub 2:23.
Karya: Ba za mu iya sanin Allah ba domin yana da wuyar fahimta.
Gaskiyar batun: A gaskiya akwai abubuwan da ba za mu iya fahimta game da Allah ba, alal misali, kasancewarsa ruhu. Amma hakan ba zai hana mu sanin Allah ba. Littafi Mai Tsarki ya ce wajibi ne mu san shi idan muna so mu sami rai na har abada. (Yohanna 17:3) A cikin Littafi Mai Tsarki, an yi amfani da kalmomin da za mu iya fahimta wajen bayyana mana abubuwa game da Mahaliccinmu, kamar halayensa, abin da yake da shi a zuciya don ’yan Adam da kuma duniya, da kuma ka’idodinsa. (Ishaya 45:18, 19; 1 Timoti 2:4) Kamar yadda muka ambata a baya, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana sunan Allah. (Zabura 83:18) Da wadannan bayanan, za mu iya sanin Allah kuma mu kusace shi.—Yakub 4:8.
a Idan kana so ka ga halittun da suka nuna cewa Allah mai hikima ne, ka duba jerin talifofin nan “Halittarsa Aka Yi?”
b Mutane da yawa sun yarda cewa sunan nan Jehobah ko Yahweh yana nufin “Yana Sa Ya Kasance.” Yadda Allah ya gaya mana sunansa kamar dai yana ce mana ne, ‘Zan cika duk wani alkawarin da na yi kuma zan yi abin da nake so.’
c Ka duba talifin nan, “Me Ya Sa Ya Kamata In Yi Addu’a? Allah Zai Ji Addu’ata Kuwa?”
d Don karin bayani, ka kalli bidiyon nan, Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki?
e Ka duba jerin talifofin nan, “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane.”