Shin Akwai Allah?
Amsar Littafi Mai Tsarki
E, Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa akwai Allah. Littafi Mai Tsarki ya karfafa mu mu yi “amfani da hankalinmu” da kuma ‘ganewarmu,’ don mu ga tabbaci cewa akwai Allah, ba kawai mu bi abin da addinai suke fadi ido rufe ba. (Romawa 12:1, New World Translation; 1 Yohanna 5:20) Ga wasu abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya fada game da wannan batun:
Irin tsarin da abubuwan da suke sama da kasa suke da shi ya nuna cewa akwai Mahalicci. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma Allah ne ya gina kome.” (Ibraniyawa 3:4) Ko da yake kwatancin nan yana da saukin fahimta, yana burge masana da yawa. a
Dukanmu ’yan Adam muna so mu san yadda za mu yi rayuwa mai kyau da kuma abin da ya sa muke wanzuwa. Abubuwa ne da muke so mu sani ko da muna da abin biyan bukata na yau da kullum. Muna bukata mu san Allah kuma mu bauta masa. Kuma Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa za mu iya zama aminansa. (Yakub 2:23; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11) Yadda muke so mu san abubuwa game da Allah ya nuna cewa akwai Allah; shi Mahalicci ne da yake kaunarmu kuma yana so mu san game da shi.—Matiyu 4:4.
Akwai annabce-annabcen da aka yi a Littafi Mai Tsarki darurruwan shekaru kafin su cika, kuma sun cika daidai yadda aka ce. Yadda annabce-annabcen nan suka cika babu kuskure ya nuna cewa ba dan Adam ba ne ya yi su.—2 Bitrus 1:21.
Marubutan Littafi Mai Tsarki sun san abubuwa game da kimiyya da mutane a zamaninsu ba su sani ba. Alal misali, a dā mutane sun yi imani cewa duniya tana a kan wata dabba, kamar giwa ko aladen daji ko shanun daji. Akasin hakan, Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya “rataya duniya babu kome a karkashinta.” (Ayuba 26:7) Kari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya ce siffar duniya tana kama ne da “kwallo.” (Ishaya 40:22, New World Translation) Mutane da yawa sun yarda cewa babu yadda marubutan Littafi Mai Tsarki za su fahimci abubuwan nan tun zamanin dā, in ba Allah ne ya bayyana musu ba.
Littafi Mai Tsarki ya amsa tambayoyi da dama da mutane ba su fahimta ba. Rashin samun amsoshin irin tambayoyin nan yakan sa wasu mutane su soma cewa babu Allah. Alal misali, idan Allah yana kaunarmu kuma shi ne mai iko duka, me ya sa duniya ta cika da mugunta da kuma wahala? Me ya sa an fi yin abubuwa marasa kyau da sunan addini maimakon masu kyau?—Titus 1:16.
a Alal misali, wani masanin taurari mai suna Allan Sandage ya taba cewa: “Na san cewa ba zai yiwu abubuwa masu tsari su fito haka kawai ba. Dole ne akwai wani abin da ya sa suka kasance haka. Ban fahimci yadda Allah yake wanzuwa ba, amma abubuwan da muke gani sun nuna cewa akwai wanda ya yi su.”