Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Giya? Shin Shan Giya Laifi Ne?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Ba zunubi ba ne mutum ya sha giya daidai wa daida. Littafi Mai Tsarki ya ce giya kyauta ce da Allah ya ba wa ’yan Adam don su ji dadin rayuwa. (Zabura 104:14, 15; Mai-Wa’azi 3:13; 9:7) Kari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa za a iya yin magani da giya.—1 Timotawus 5:23.
Yesu ya sha giya lokacin da yake duniya. (Matta 26:29; Luka 7:34) Wata sananniyar mu’ujiza da Yesu ya yi ita ce juya ruwa zuwa giya, kuma ya yi hakan ne don ya taimaka a wurin bikin aure.—Yohanna 2:1-10.
Matsalolin shan giya fiye da kima
Littafi Mai Tsarki ya ce giya tana da amfani a wasu fannoni, amma ya haramta buguwa da giya. Saboda haka, ya kamata duk Kirista da ya zabi ya sha giya ya yi hakan daidai wa daida. (1 Timotawus 3:8; Titus 2:2, 3) Littafi Mai Tsarki ya ba da dalilai da ya kamata mu guje wa shan giya fiye da kima.
Yana hana mutum yin tunani da kuma yanke shawara mai kyau. (Misalai 23:29-35) Mutumin da ya bugu ba zai iya bin dokar Littafi Mai Tsarki da ta ce “ku mika jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karba ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi.”—Romawa 12:1, Littafi Mai Tsarki.
Shan giya da yawa zai sa mutum keta iyakarsa kuma zai ‘kawar da hankalinsa’ ko kuma ya hana shi yin abin da ya dace.—Hosiya 4:11; Afisawa 5:18.
Yana jawo talauci da kuma rashin lafiya.—Misalai 23:21, 31, 32.
Shan giya da yawa da buguwa suna bata wa Allah rai.—Misalai 23:20; Galatiyawa 5:19-21.
Yaya za ka san ko ka wuce kima?
Za a iya ce mutum ya sha giya da yawa idan giyar da ya sha za ta iya jefa shi ko wasu cikin hadari. A cikin Littafi Mai Tsarki, an nuna cewa ba sai mutum ya fita hankalinsa kafin a san cewa ya bugu ba. Idan mutum ya kasa tara hankalinsa a wuri daya ko ya kasa tafiya da kyau ko yana yawan fada ko kuma ba ya iya magana da kyau, hakan zai nuna cewa ya bugu. (Ayuba 12:25; Zabura 107:27; Misalai 23:29, 30, 33) Wadanda ba sa buguwa ma “zukatanku” za su iya yin “nauyi da ... maye” kuma hakan zai jawo musu munanan sakamako.—Luka 21:34, 35.
Guji shan giya gaba daya
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa akwai lokuta da ya kamata Kirista ya daina shan giya gaba daya, wadannan lokutan su ne:
Idan shan giya zai sa wasu tuntube.—Romawa 14:21.
Idan shan giya ya saba wa dokar kasar.—Romawa 13:1.
Idan mutum ba zai iya ce wa kansa ya isa ba da zarar ya soma shan giya. Ya kamata wadanda suke fama da maye su dauki mataki nan da nan.—Matta 5:29, 30.