Labarai na Kai Bakin Mutuwa—Mene ne Yake Nufi?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Mutane da yawa da suka tsallake rijiya da baya suka ce sun rabu da jikinsu kuma suka shiga cikin wani wuri mai kyaun gaske. Littafin nan Recollections of Death ya ce: ‘Wadansun su suna daukan wannan wata gata ce ta musamman su yi rayuwa a wata duniya.” Littafi Mai Tsarki bai ambata irin wannan aukuwa ba, amma ya fadi gaskiya cewa hakan ba wahayin wata rayuwa ba ce.
Matattu ba su san kome ba.
Littafi Mai Tsarki ya ce matattu “ba su san kome ba.” (Mai-Wa’azi 9:5) Idan mutum ya mutu ba ya zuwan wani waje ko soma wani tunani ba. Koyarwar cewa kurwa marar mutuwa ce ba daga Littafi Mai Tsarki ba ne. (Ezekiel 18:4) Saboda haka, babu wani labari na tsallake rijiya da baya da ya nuna cewa ya faru a sama, ko hell, ko kuma a wani wajen rayuwa bayan mutuwa ba.
Li’azaru ya fadi wani abu ne cewa ya rayu bayan da ya mutu?
Labarin Littafi Mai Tsarki game da Li’azaru ya kwatanta mutuwa sarai: Yesu ya ta da shi bayan kwana hudu da mutuwa. (Yohanna 11:38-44) Da a ce Li’azaru yana more rayuwa a wani wuri dabam ne da zai zama mugunta ne Yesu ya tashe shi ya sake rayuwa a duniya. Amma, babu wani labari daga Li’azaru game da wata rayuwa bayan mutuwa ba. Da hakan ya faru, babu shakka da Li’azaru ya yi tadin rayuwar da ya yi sa’ad da ya mutu. Abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda Yesu ya kwatanta mutuwar Li’azaru da barci, yana nuna cewa sa’ad da ya mutu, bai san kome ba sam.—Yohanna 11:11-14.