Akwai Wanda Ya San Ainihin Waɗanda Suka Rubuta Littafi Mai Tsarki Kuwa?
Amsar Littafi Mai Tsarki
An sanar da mutane da yawa cewa ba za mu taɓa sanin ainihin waɗanda suka rubuta Littafi Mai Tsarki ba. Amma Littafi Mai Tsarki ya bayyana sarai waɗanda suka rubuta abin da ke ciki. An soma wasu rubutun da furuci kamar irin waɗannan “labarin Nehemiah,” “ru’ya ke nan ta Ishaya,” da kuma “maganar Ubangiji wadda ta zo wurin Joel.”—Nehemiah 1:1; Ishaya 1:1; Joel 1:1.
Yawancin marubutan Littafi Mai Tsarki sun yarda cewa sun rubuta a cikin sunan Jehobah ne, Allah ɗaya na gaskiya, kuma shi ne ya yi musu ja gora. Annabawa da suka rubuta Nassosin Ibrananci sun sanar fiye da sau 300 cewa: “Hakanan Ubangiji ya faɗi.” (Amos 1:3; Mikah 2:3; Nahum 1:12) Wasu marubutan sun sami saƙon Allah ta wurin mala’iku.—Zechariah 1:7, 9.
Mazaje 40 ne suka rubuta Littafi Mai Tsarki cikin tsawon shekaru 1,600. Wasu cikinsu sun rubuta fiye da littafi guda cikin Littafi Mai Tsarki. Hakika, Littafi Mai Tsarki ƙaramin laburare ne mai ɗauke da littattafai 66. Yana ɗauke da littattafai 39 na Nassosin Ibrananci, da yawanci mutane ke kira Tsohon Alkawari, da kuma littattafai 27 na Nassosin Helenanci na Kirista, da ake yawan kiransu Sabon Alkawari.