Koma ka ga abin da ke ciki

Gidan wani dan’uwa da mahaukaciyar guguwar ta lalata

18 GA NUWAMBA, 2019
Japan

Mahaukaciyar Guguwar Bualoi Ta Yi Barna a Jafan

Mahaukaciyar Guguwar Bualoi Ta Yi Barna a Jafan

A ranar 25 da 26 ga Oktoba, 2019, mahaukaciyar guguwar Bualoi ta yi barna a gabashin kasar Jafan. Mahaukaciyar guguwar Bualoi ce guguwa ta uku da ta farma gabashin Jafan tun watan Satumba, sai kuma guguwar Faxai da Hagibis. Wannan mahaukaciyar guguwar ta sa koguna su cika kuma suka jawo ambaliya mai tsanani a wasu yankuna. Akalla gidajen 81 na ’yan’uwa sun lalace. Babu wani dan’uwa da ya rasa ransa amma wata ’yar’uwa ta ji rauni. ’Yan’uwanmu da ke yankin Chiba sun sha wahala sanadiyyar guguwa guda uku da suka adabi kasar Jafan.

Kwamitin Ba da Agaji guda uku ne aka kafa a wuraren da mahaukaciyar guguwar Faxai da Hagibis suka yi banar. Ban da haka, Kwamitin Ba da Agaji tana tallafa wa mutanen da mahaukaciyar guguwar Bualoi ta shafa. Ofishinmu da ke Jafan na taimaka wa Kwamitin Ba da Agaji don su tallafa wa ’yan’uwa ta wajen share da tsabtacce mahalli da kuma gyara gidajen da suka lalace. Masu kula da da’ira suna tsara yadda za a karfafa ’yan’uwa maza da mata a yankuna.

A wannan mawuyacin lokacin muna yi wa ’yan’uwanmu a Jafan addu’a kuma muna da tabbaci cewa Jehobah zai kula da bayinsa da suka kusan “fid da zuciya” saboda wannan bala’i.​—Zabura 34:18.