8 GA YULI, 2016
Sri Lanka
Shaidun Jehobah Sun Kai Agaji Bayan An Yi Ambaliyar Ruwa a Siri Lanka
COLOMBO, Siri Lanka—Wata ambaliyar laka ta shigo kauyukan birnin Aranayaka, a jihar Siri Lanka da ke da nisan kilomita 100 daga Colombo babban birnin Siri Lanka. Ambaliyar ta kashe mutane fiye da 100 kuma ta halaka gidaje wajen 350,000. Hakan ya faru ne sa’ad da aka yi awa 24 ana ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranar 15 ga Mayu a garin Kilinochchi. Hukuma ta ce tun bayan ambaliyar ruwa da aka yi a 2004, wannan ya fi dukan sauran bala’in da suka faru a Siri Lanka.
Ofishin Shaidun Jehobah da ke Siri Lanka ya ce, babu wani Mashaidin Jehobah da ya mutu, amma kusan guda 200 sun rasa gidajensu. Ambaliyar ruwan ta rufe Majami’ar Mulki ko kuma wurin ibada a Kaduwela da ke da nisan kilomita 15 daga Colombo kuma ruwan ya kai wajen kafa 6.
Nan da nan, sai Shaidun Jehobah suka tura masu kai kayan agaji don su kula da kuma taimaka wa wadanda bala’in ya shafa. An yi amfani da Majami’ar Mulkin da ke Kotahena wajen ajiye abubuwa kamar ruwan sha da tufafi da kuma magunguna. Shaidun Jehobah da yawa da ke yankin sun ba da kansu don su rarraba wadannan abubuwan ga ’yan’uwansu da kuma makwabta.
Wani kakakin Shaidun Jehobah a Siri Lanka mai suna Nidhu David ya ce: “Za mu ci gaba da yin addu’a a madadin iyalan da wannan bala’in ya shafa. Kuma muna kan taimaka wajen share gidajen da suka lalace da kuma ba mutane da bala’in ya shafa abinci da tufafi. Yadda ’yan’uwanmu suka ba da kansu don su taimaka ya karfafa mutane sosai a wannan lokacin.”
Media Contacts:
International: David A. Semonian, Office of Public Information, 1-718-560-5000
Sri Lanka: Nidhu David, 94-11-2930-444