Koma ka ga abin da ke ciki

8 GA SATUMBA, 2017
AMIRKA

Rahoto game da mahaukaciyar guguwar Irma

Rahoto game da mahaukaciyar guguwar Irma

Mahaukaciyar guguwar teku da aka soma a ranar 5 ga Satumba, 2017, ne daya daga cikin guguwa mafi karfi da aka taba gani a yankin Atlantika. Guguwar ta riga ta yi barna sosai a tsibiran da ke yankin Caribbean. Babu wani dan’uwa da aka ba da rahoto cewa ya ji rauni ko ya rasa ransa a guguwar. Amma guguwar ta lalata Majami’ar Mulki a tsibirin La Désirade da Guadeloupe da kuma tsibirin St. Barts. Kari ga haka, guguwar ta lalata Majami’ar Babban Taro da ke tsibirin St. Martin.

Tsibirin Barbuda ne mahaukaciyar guguwar ta fi yin barna sosai, kuma kimanin mutane kashi hamsin bisa dari ne gidajensu ya halaka. Gwamnati ta umurci Jama’ar da ke tsibirin, har da ’yan’uwanmu guda 11, cewa su bar tsibirin don ana sa ran wata mahaukaciyar guguwa ta José za ta kara auku a yankin Caribbean a karshen mako.

’Yan’uwa suna kokarin yin tanadin kayan agaji yayin da mahaukaciyar guguwar take kokarin shiga tsibirin Bahamas da Kuba da kuma kudanci Amirka. ’Yan’uwan suna kokarin neman masauki ma ’yan’uwan da watakila guguwar za ta halaka gidajensu.

Media Contact:

David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000