Koma ka ga abin da ke ciki

21 GA SATUMBA, 2017
PUERTO RICO

Rahoto Game da Abin da Ya Faru Bayan Aukuwar Mahaukaciyar Guguwar Maria

Rahoto Game da Abin da Ya Faru Bayan Aukuwar Mahaukaciyar Guguwar Maria

A rana Laraba 20 ga Satumba, 2017, mahaukaciyar guguwa mai suna Maria ta auku a Amirka. Wannan guguwa ita ce na biyar mafi karfi da suka taba auku, kuma ta yi kacakaca da tsibirin Puerto Rico. Don haka, tsibirin gabaki daya babu wutan lantarki kuma gwamnati ta kafa dokar kada a wuce karfe 6:00 na yamma a waje.

Babu wani rahoto cewa wani dan’uwa ya mutu ko ji rauni. Yanzu haka an kokarin tura kayan agaji wurin. ’Yan’uwan za su rika kwana a Majami’ar Mulkin bai halaka ba kuma zai zama wurin raba kayan agaji.

Guguwar ta dan yi barna a Ofishinmu da ke birnin San Juan. Amma an ba da rahoto cewa babu abin da ya faru da ’yan’uwan da ke wurin. A yanzu haka ’yan’uwan da ke wurin ba za su iya yin amfani da yanar gizo ba, kuma ana yin amfani da janareto don samu wutan lantarki.

Babu shakka, mun san cewa ’yan’uwan da ke wurin za su sami karfafa don yadda kungiyar Jehobah ke kokarin tallafa musu ta wurin tura kayan agaji.​—2 Kor. 1:31.

Media Contact:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000