Koma ka ga abin da ke ciki

23 GA SATUMBA, 2020
RASHA

Ana So A Jefa Dan’uwa Yuriy Zalipayev a Gidan Yari na Tsawon Shekara Biyu a Rasha

Ana So A Jefa Dan’uwa Yuriy Zalipayev a Gidan Yari na Tsawon Shekara Biyu a Rasha

Ranar da Za A Yanke Hukuncin

A ranar 7 ga Oktoba, 2020, * Kotun Gundumar Mayskiy da ke Jamhuriyar Kabardino-Balkarian zai sanar da hukuncin da ya yanke a kan karar da aka shigar game da Dan’uwa Yuriy Zalipayev. Za a iya jefa shi a kurkuku na tsawon shekara biyu.

Karin Bayani

Yuriy Zalipayev

  • Shekara Haihuwa: 1962 (Samara)

  • Tarihi: Ya taba yin aikin welda da direban babban mota. Yana son yin wakoki da kuma hawan tuddai

  • Ya auri Natalia a shekara ta 1983, sun yi aji daya a lokacin da suke yara. Bayan sun yi shekaru goma da aure, sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Suna da yara uku kuma dukansu suna bauta wa Jehobah, har ma da wasu danginsu

Yadda Labarin Ya Soma

A ranar 20 ga Agusta, 2016, wasu jami’an tsaro sun shiga wani Majami’ar Mulki a garin Mayskiy, kuma suka boye wasu littattafanmu da gwamnati ta ce suna dauke da “tsattsaurar ra’ayi.” Sun yi hakan ne domin su zargi ’yan’uwanmu da aikata laifi. Ko da yake ’yan’uwanmu suna da bidiyon da ya nuna cewa jami’an tsaron ne suka boye littattafan, wani kotu ya ce ’yan’uwanmu sun taka doka kuma ya ci wa ’yan’uwan da ke yankin tarar dala 2,634 (wajen naira 1,004,344). Watanni bayan hakan, an zargi Dan’uwa Zalipayev da aikata laifi don abin da ya faru a ranar.

Wadanda suka shigar da karar sun ce Dan’uwa Zalipayev ya rarraba littattafai masu tsattsauran ra’ayi kuma ya karfafa wasu Shaidun Jehobah su yi fada da wadanda suke bin wasu addinai dabam. Doka ta haramta irin wannan halin kuma yana “sa mutane su kasance da tsattsauran ra’ayi” (Bisa ga dokar Rasha da ke, Part 1 of Article 280 of Russia’s Criminal Code).

Kotu ya fara sauraron karar a ranar 21 ga Yuni, 2020. Yayin da ake sauraron karar, shaidun wadanda suka shigar da karar sun yi ta ba da shaidar da ba ta jitu da na junansu ba, kuma sun yi ta fadin abubuwan da ba su da hujja a kai. Alal misali, wasu shaidun da suka ce sun ji Dan’uwa Zalipayev a wurin taron yana zuga Shaidun Jehobah su yi fada da mutane, ba sa wurin taron a lokacin. Kari ga haka, wasu daga cikin shaidun masu shigar da karar sun amince cewa jami’an tsaro ne suka boye littattafan a Majami’ar Mulkin.

Yayin da Dan’uwa Zalipayev yake jiran hukuncin da za a yanke, addu’armu ita ce, shi da iyalinsa su sami karfin gwiwa da kuma kwanciyar hankali daga kalmomin Dauda da ya ce: “Yahweh ne karfina da garkuwata, zuciyata ta dogara gare shi. Ya taimake ni, zuciyata ta yi farin ciki.”​—Zabura 28:7.

^ sakin layi na 3 Za a iya canja ranar