7 GA OKTOBA, 2020
RASHA
Kotu Ya Wanke Dan’uwa Yuriy Zalipayev Daga Zargi!
A ranar 7 ga Octoba, 2020, Kotun Gundumar Mayskiy da ke Jamhuriyar Kabardino-Balkarian, ya gano cewa Dan’uwa Yuriy Zalipayev bai yi wani laifi ba, kuma kotun ya wanke shi daga dukan zargin da aka yi masa. Wanda ya shigar da karar yana da izini ya daukaka karar a cikin kwanaki goma masu zuwa.
Wanda ya shigar da karar ya ce Dan’uwa Zalipayev ya iza ’yan’uwansa Shaidun Jehobah su yi fada da mutane. Amma mutane fiye da 30 sun ba da shaida cewa bai yi hakan ba, sun ce abin da ya yi shi ne, ya karfafa mutane su karanta Littafi Mai Tsarki, su mutunta kowa, kuma su yi wa kowa alheri.
Abin da wata kungiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke kāre hakkin wadanda aka tsare su ba bisa doka ba, wato UN Working Group on Arbitrary Detention, ta fada ne ya kara sa kotun ya wanke dan’uwan daga zargi. Kungiyar ta bayyana sarai cewa Shaidun Jehobah ba sa yin fada kuma ba sa goyon bayan duk wani abin da zai kai ga tashin hankali.
Da aka sanar da cewa ba shi da laifi, Dan’uwa Zalipayev ya ce: “Dā ma dangina da abokaina suna a shirye su amince da duk hukuncin da za a yanke, kome muninsa. Godiya ga Jehobah, domin har a lokacin da ake saurarar karar, ban ji tsoro ba. Ina farin ciki sosai kuma na gode wa dukan wadanda suka ba da shaida cewa ban yi wani laifi ba.”