20 GA NUWAMBA, 2020
RASHA
Mai Yiwuwa A Yanke wa Dan’uwa Sergey Ledenyov Hukuncin Yin Shekara Shida a Kurkuku a Rasha
Hukuncin da Za A Yanke
A ranar 24 ga Nuwamba, 2020, * Kotun Birnin Petropavlovsk-Kamchatskiy da ke Yankin Kamchatka zai sanar da hukuncinsa a kan Dan’uwa Sergey Ledenyov. Za a iya daure shi a kurkuku har tsawon shekara shida.
Karin Bayani
Sergey Ledenyov
Shekarar Haihuwa: 1974 (Ossora, a Yankin Kamchatka)
Tarihi: Yana da ’yan’uwa biyar. Yana son yin zane da kuma daukan hoto. Shi magini ne da kuma mai saka tiles. Kafin ya soma nazari da Shaidun Jehobah, ya dauka cewa Littafi Mai Tsarki tsohon littafi ne kuma bai jitu da koyarwar kimiyya ba. Ya auri matarsa mai suna Anna a 2017. Anna ta ce bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki ne ya sa maigidanta Sergey ya zama natsattsen mutum, mai kula da iyalinsa da kuma mai kauna
Yadda Labarin Ya Soma
A ranar 2 ga Disamba, 2018, wasu jami’an tsaro dauke da makamai da kuma fuskokinsu a rufe sun shiga gidan Dan’uwa Ledenyov a Petropavlovsk-Kamchatskiy. Sun dauke shi kuma sun kama shi da laifi a karkashin Shafi na 282.2 a kundin tsarin dokoki da suka shafi aikata laifi a Rasha. An soma sauraron shari’ar a ranar 28 ga Nuwamba, 2019.
A ranar 12 ga Disamba, 2019, Kotun Birnin Petropavlovsk-Kamchatskiy da ke Yankin Kamchatka ya mai da karar Dan’uwa Sergey Ledenyov hannun wanda ya shigar da karar. Wannan yana yawan faruwa ne idan kotun ya gano cewa babu hujjar da za ta goyi bayan karar da aka shigar. Amma a ranar 4 ga Fabrairu, 2020, wani kotun da ya fi wannan ya dakatar da matakin da wannan karamin kotun ya dauka kuma ya sa aka ci gaba da sauraron karar. Bayan haka, yayin da hukumomi suke yi wa matar Dan’uwa Ledenyov da wata ’yar’uwa tambayoyi, sun yi kokarin tilasta musu su ba da shaidar karya a kan Dan’uwa Ledenyov. Amma su biyun sun ki su yi hakan.
Dangin Dan’uwa Ledenyov da ba Shaidun Jehobah suna mamakin yadda ake tsananta masa don imaninsa.
Muna addu’a a madadin Dan’uwa Ledenyov da matarsa yayin da suke jiran hukuncin da za a yanke. Muna da tabbaci cewa ruhun Jehobah yana tare da su.—1 Bitrus 4:14.
^ sakin layi na 3 Za a iya canja ranar.