Koma ka ga abin da ke ciki

Dan’uwa Anatoliy Tokarev a gaban Kotu a watan Agusta 2020

23 GA OKTOBA, 2020
RASHA

Wani Kotu a Rasha Ya Ci Wa Dan’uwa Anatoliy Tokarev Tara

Wani Kotu a Rasha Ya Ci Wa Dan’uwa Anatoliy Tokarev Tara

A ranar 23 ga Oktoba, 2020, Kotun Gundumar Oktyabrsky da ke Birnin Kirov ya kama Dan’uwa Anatoliy Tokarev da laifi kuma ya ci masa tarar dala 6,552 (wajen naira 2,499,195). An ba shi kwana goma ya daukaka kara idan yana so.

Da yake maganarsa ta karshe a kotun, Dan’uwa Tokarev ya yi karfin zuciya kuma ya gaya musu cewa: “A batun wannan zargin, abin da jami’an tsaro suka yi mini yana kamar suna gaya mini ne cewa: ‘Ko ka musunci imaninka, ko . . . a yi maka hukunci mai tsanani a gaban jama’a.’” Ya ci gaba da cewa, “Ya Mai Girma, a rana ta farko da aka saurari wannan karar, akwai abin da na fada, kuma zan kara maimaitawa, ni ba zan taba yin musun imanina ba. . . . Hakika, idan aka ce za a jefa ni a kurkuku ko a kashe ni, zan ji tsoro, kamar yadda duk wani Mashaidin Jehobah ma zai ji, kuma yadda ake cewa ni mai tsattsaurar ra’ayi ne ba karamin bata suna ba ne a gaban jama’a, don ba abin da na yi. Duk da haka ya Mai Girma, ba zan iya daina bauta wa Allah kuma in sa ya daina kauna ta ba.”