28 GA OKTOBA, 2020
RASHA
Wani Kotu a Rasha Ya Hana A Saki Dan’uwa Bazhenov da Wuri
A ranar 28 ga Oktoba, 2020, Kotun Birnin Dimitrovgrad da ke Yankin Ulyanovsk ya hana a saki Dan’uwa Konstantin Bazhenov daga kurkuku kafin lokacin da aka kayyade masa kuma a ci masa tara a maimakon lokacin da zai zauna a kurkuku. Kotun ya ba shi kwana goma ya daukaka kara idan yana so.
A watan Yuni 2018 ne aka kai Dan’uwa Bazhenov kurkuku yayin da yake jiran hukuncin da za a yi masa, kuma a lokacin ya ji tsoro. Amma da yake kurkuku, ya soma rubuta nasossi da ya tuna a wata takarda, har ya rubuta ayoyi wajen 500. Daga baya ya samo Littafi Mai Tsarki kuma ya karance shi cikin watanni hudu. Dan’uwa Bazhenov ya rubuta wasiku ga matarsa da abokansa don ya karfafa su da abin da ya karanta. Ya dinga rera wakokinmu kuma ya yi ta rokon Jehobah ya taimaka masa.
Dan’uwa Bazhenov ya yi fiye da kwana 340 yana tsare kafin a yi masa hukunci. Bayan kotu ya kama shi da laifi kuma ya yanke masa hukuncin yin shekara uku da rabi a kurkuku a watan Satumba 2019, ya ci gaba da yin wadannan ayyukan ibada. Godiya ga Jehobah, domin Dan’uwa Bazhenov ya samu ya yi bikin Tuna da Mutuwar Yesu a kurkukun. Dangantaka ta kud da kud da yake da ita da Jehobah ta taimaka wa Dan’uwa Bazhenov ya ci gaba da yin farin ciki yayin da yake jimre tsanantawar nan. Za mu rika tuna da Dan’uwa Bazhenov a addu’o’inmu.