8 GA OKTOBA, 2020
RASHA
Wani Kotu a Rasha Ya Kama Shaidun Jehobah Shida da Laifi Kuma Ya Hukunta Cewa Za A Rika Sa Musu Ido
A ranar 8 ga Oktoba, 2020, Kotun Gundumar Zasviyazhsky a Birnin Ulyanovsk ya kama ’yan’uwan nan da laifi, wato Dan’uwa Aleksandr Ganin da Khoren Khachikyan da Andrey Tabakov da Mikhail Zelenskiy da Kuma Dan’uwa Sergey Mysin da matarsa Nataliya. Za a yi shekara biyu da wata shida zuwa shekara hudu ana sa musu ido. Hakan ya dangana da hukuncin da aka yanke wa kowannensu. Wannan yana nufin cewa ba za a kai wadannan ’yan’uwanmu kurkuku ba.