26 GA OKTOBA, 2020
RASHA
Wani Kotu a Rasha Ya Sake Hana A Saki Dan’uwa Christensen da Wuri
A ranar 26 ga Oktoba, 2020, Kotun Gundumar Lgov ya sake hana a saki Dan’uwa Dennis Christensen, wanda ya riga ya yi fiye da shekara uku a kurkuku. Zai iya daukaka kara cikin kwana goma. Wa’adin hukuncin da aka yanke wa Dan’uwa Christensen zai kare ne a watan Mayu 2022. Hakan zai yiwu idan aka hada lokacin da ya yi a daure kafin a yanke masa hukunci. Amma a watan da ya shige, mahukuntan kurkuku sun yi masa sharri cewa “yana yawan taka” dokokin kurkukun. Don haka, za a iya cire lokacin da ya yi a daure kafin a yanke masa hukunci, kuma idan aka yi haka, ba zai fito a Mayu 2022 ba.
Tun da aka kama Dan’uwa Christensen a ranar 25 ga Mayu 2017, shi da matarsa, Irina, sun jimre da matsaloli iri-iri. Duk da haka, suna jimre matsalolinsu da farin ciki, kuma hakan ya yiwu ne don addu’o’in da miliyoyin ’yan’uwanmu suke yi a duk fadin duniya.