Koma ka ga abin da ke ciki

13 GA AFRILU, 2016
RASHA

Masu Mulki a Kasar Rasha Suna Yunkurin Dakatar da Kungiyoyin Shaidun Jehobah a Kasar

Masu Mulki a Kasar Rasha Suna Yunkurin Dakatar da Kungiyoyin Shaidun Jehobah a Kasar

A yankuna dabam-dabam, masu mulki a kasar Rasha suna takura wa Shaidun Jehobah kuma suna da’awar cewa ibadarsu ayyukan “tsattsauran ra’ayi” ne.

  • Tyumen, a Yankin Tyumen. Mai shigar da kara a yankin ya kaga wa wani Mashaidin Jehobah laifin “rarraba littattafai masu tsattsauran ra’ayi.” Bayan da aka kama Mashaidin da laifi, mai shigar da karar ya nemi a dakatar da kungiyar Shaidun Jehobah da aka yi rijistar a yankin Tyumen. Kotun Koli na Kasar Rasha zai saurari wannan karar a ranar 14 ga Afrilu, 2016.

  • Elista, a Jamhuriyar Kalmykia. Wani shugaban ’yan sanda ya ba da oda a bincika wata Majami’ar Mulki a Elista, inda aka “gano” wani littafin Shaidun Jehobah da ke cikin jerin littattafai masu koyar da tsattsauran ra’ayi da kasar ta fitar. Da wannan shaidar, wato, wannan littafin da aka yi cuwa-cuwa aka saka a cikin Majamiyar Mulki, mai shigar da kara a madadin Jamhuriyar Kalmykia ya nemi hanyar dakatar da kungiyar Shaidun Jehobah da aka yi rijistar a Elista. Ana jiran ranar da za a saurari karar a Kotun Koli na Kasar Rasha.

  • Akwai kuma wasu kararraki da aka shigar game da dakatar da kungiyoyin Shaidun Jehobah a wurare kamar Stariy Oskol da kuma Belgorod kuma ana jiran ranar da za a saurari kararrakin a Kotun Koli na Rasha.