Koma ka ga abin da ke ciki

21 GA YUNI, 2017
RASHA

Bidiyon da Ya Nuna Yadda Hukumomin Rasha Suka Kai Hari a Wurin Taron Shaidun Jehobah

Bidiyon da Ya Nuna Yadda Hukumomin Rasha Suka Kai Hari a Wurin Taron Shaidun Jehobah

NEW YORK​—An nuna wani bidiyo kwanan nan a talabijin na glavny.tv, inda ’yan watsa labaru a Central Federal District of Russia sun nuna yadda wasu ’yan sandan Rasha dauke da makamai, da kuma hukumar Federal Security Service (FSB) suka kai hari wa Shaidun Jehobah a wurin taronsu a Oryol da ke Rasha a ranar 25 ga Mayu, 2017.

Hukumomin Rasha sun kai wa Shaidun Jehobah hari a wurin taron ibada da suke yi a ranar 25 ga Mayu, 2017 a Oryol da ke Rasha.

An nuna wani dan Denmark mai suna Dennis Christensen a bidiyon yana tattaunawa da hukumomin cikin kwanciyar hankali. Hukumar ta kama shi lokacin da suka kai harin kuma har yanzu yana tsare.

Dennis Christensen, wani dan Denmark kuma dattijo ne a ikilisiyar Shaidun Jehobah yana tattaunawa da hukumomin. Hukumar FSB ta tsare shi tun ranar 25 ga Mayu, 2017.

David A. Semonian, kakakin Shaidun Jehobah a hedkwatarsu ya ce: “Wannan bidiyon ya nuna halin lumana da Shaidun Jehobah suke da shi duk da cewa hukumomin sun yi barazana da kuma tsoratar da su don su katse nazarin Littafi Mai Tsarki da suke yi. Ba za a daina wannan cin mutuncin ba har sai Kotun Kolin Rasha ya canja hukuncin da ya yanke game da Shaidun Jehobah. Mun damu kwarai game da yanayin da dan’uwanmu Dennis Christensen yake ciki, domin hukumar ta ki a ziyarce shi ko ma ya amsa waya daga matarsa. Muna fatan cewa za a sake shi nan ba da dadewa ba.”

Inda Aka Samo Labarin:David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000