RAYUWAR KIRISTA
Ku Gayyaci Kowa a Yankinku Zuwa Taron Tuna da Mutuwar Yesu!
Za mu soma kamfen na gayyatar mutane zuwa taron Tuna da Mutuwar Yesu a ranar 27 ga Fabrairu, kuma muna son mutane da yawa su halarci taron. Zai dace mu koma ziyara wurin mutanen da suka saurare mu.
DABARUN DA ZA A YI AMFANI DA SU
KA YI GABATARWARKA
“Muna rarraba takardun nan don mu gayyaci mutane zuwa wani taro na musamman. Miliyoyin mutane a duniya za su taru ranar 23 ga Maris don su Tuna da Mutuwar Yesu kuma su ji jawabin Littafi Mai Tsarki da ya nuna yadda muke amfana daga mutuwarsa. An rubuta lokaci da kuma wurin da za a yi taron a wannan yankin a cikin takardar. Za mu so ka halarci taron.”
Idan mutumin ya saurara . . .
-
KA BA DA HASUMIYAR TSARO
Ka yi shirin koma ziyara.
-
KA NUNA BIDIYON TUNA MUTUWAR YESU
Ka yi shirin koma ziyara.
Idan ka koma za ka iya ce . . .
-
KA NUNA ME YA SA ZAI DACE MU YI NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI?
Sai ka ba da littafin da muke nazari da shi.
-
KA BA DA MENENE AINIHI LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA?
Ka yi amfani da shafuffuka na 206-208, wajen tattauna wasu abubuwa game da taron Tuna Mutuwar Yesu. Bayan haka, ka ba da littafin.
-
KA BA DA KA SAURARI ALLAH
Ka yi amfani da shafuffuka na 18-19 wajen tattauna amfanin fansar Kristi. Bayan haka, ka ba da ƙasidar.