9- 15 ga Janairu
ISHAYA 29-33
Waƙa ta 123 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Wani Sarki Za Ya Yi Mulki Cikin Adalci”: (minti 10)
Ish 32:1
—Yesu ne Sarkin da zai yi mulki cikin adalci (w14 2/15 6 sakin layi na 13) Ish 32:2
—Yesu ya naɗa hakimai da za su kula da tumakinsa (ip-1-E 332-334 sakin layi na 7-8) Ish 32:3, 4
—Ana horar da mutanen Allah kuma ana ba su umurni da ke taimaka musu su kasance da aminci (ip-1-E 334-335 sakin layi na 10-11)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Ish 30:21
—Ta yaya Jehobah yake yi wa bayinsa ja-gora? (w14 8/15 21 sakin layi na 2) Ish 33:22
—Yaushe ne Jehobah ya zama Mai-mulki da Mai-ba da shari’a da kuma Sarkin al’ummar Isra’ila kuma a wace hanya? (w14 10/15 14 sakin layi na 4) Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya mini game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne na koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon da zan iya yin amfani da su a wa’azi?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Ish 30:22-33
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Koma Ziyara: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Bangon gaban wp17.1
—Ka karanta nassi daga na’urarka. Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) lv 31-32 sakin layi na 12-13
—Ka nuna yadda za a iya ratsa zuciyar ɗalibi.
RAYUWAR KIRISTA
Waƙa ta 119
“Wurin Fakewa Daga Iska” (Ish 32:2): (minti 9) Ka nuna bidiyon
Ku Saurara a Taro: (minti 6) Ka nuna bidiyon nan Ku Saurara a Taro. Bayan kun kalli bidiyon, sai ka gayyaci yara ƙanana zuwa kan dakali kuma ka tambaye su: Mene ne zai iya hana ku saurara a taro? Me zai faru inda a ce Nuhu bai saurari Jehobah sa’ad da yake bayyana masa yadda zai gina jirgin ba? Me ya sa yake da muhimmanci yara su riƙa saurarawa a taro?
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) kr babi na 6 sakin layi na 16-24, akwatin nan “Ka Gaskata da Mulkin Kuwa?”
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 40 da Addu’a