DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Hidimar da Lawiyawa Suke Yi
Jehobah ya zaɓi Lawiyawa su yi masa hidima maimakon duka ’ya’yan fari na Isra’ila su riƙa yin haka (L.Ƙi 3:11-13; it-2-E 683 ¶3)
Lawiyawan sun yi wasu ayyuka masu muhimmanci (L.Ƙi 3:25, 26, 31, 36, 37; it-2-E 241)
Lawiyawan sun yi aiki tuƙuru a lokacin da suke tsakanin shekara 30 da 50 (L.Ƙi 4:46-48; it-2-E 241)
Mazan da suka fito daga zuriyar Haruna ne suke yin hidimar firist. Sauran Lawiyawan kuma suna taimaka musu. Haka ma a ikilisiyar Kirista, wasu maza suna yin ayyuka masu muhimmanci, wasu kuma suna taimaka musu da yin wasu ayyuka a ikilisiya.