RAYUWAR KIRISTA
Mun Gode wa Allah da Yesu don ’Yanci da Za Mu Samu a Nan Gaba
Waɗanne matsaloli ne kake fuskanta a kowace rana? Kai magidanci ne da ke ƙoƙarin kula da iyalinka? Kai kaɗai ne ko ke kaɗai ce kike kula da iyalinki? Shin kana fuskantar cin zali daga tsararka a makaranta? Kana fama da rashin lafiya ne ko tsufa? Kowannenmu yana da matsala da yake fama da ita. Wasu ’yan’uwa ma suna fama da matsaloli da yawa a lokaci ɗaya. Duk da haka mun san cewa wata rana, Jehobah zai kawar da duka matsalolin.—2Ko 4:16-18.
Kafin lokacin, sanin cewa Jehobah ya fahimci matsalolin da muke fama da su na ƙarfafa mu sosai. Ban da haka ma, yana ɗaukan amincinmu da haƙurinmu da muhimmanci, shi ya sa ya yi alkawari cewa zai albarkace mu a nan gaba. (Irm 29:11, 12) Yesu ma ya damu da mu. Yayin da muke ci gaba da ayyukan ibada, mu tuna da abin da Yesu ya gaya mana cewa: “Ina tare da ku.” (Mt 28:20) Idan mun dakata kuma muka yi bimbini a kan ’yancin da za mu samu a Mulkin Allah, hakan zai ƙarfafa begenmu kuma ya sa mu jimre matsalolin da muke fama da su.—Ro 8:19-21.
KU KALLI BIDIYON NAN KU ZUBA IDO GA YESU YAYIN DA BABBAN HADARI YAKE GABATOWA!—ALBARKAR DA MULKIN ZA TA KAWO, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Mene ne ya ware ’yan Adam daga Allah, kuma mene ne sakamakon?
-
Waɗanne albarku ne bayin Allah masu aminci za su samu a nan gaba?
-
Me zai sa mu more waɗannan albarkun?
-
Me kake ɗokin ganin cikarsa a sabuwar duniya?