8-14 ga Fabrairu
LITTAFIN ƘIDAYA 1-2
Waƙa ta 123 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Jehobah Yana Tsara Mutanensa”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
L.Ƙi 1:2, 3—Me ya sa aka ƙirga jama’ar Isra’ila? (it-2-E 764)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) L.Ƙi 1:1-19 (th darasi na 5)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 3) Ka soma da bin bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Ka gaya wa mutumin cewa za ka so ka soma nazari da shi kuma ka gabatar da (amma kar ka kunna) bidiyon nan Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki? (th darasi na 9)
Komawa Ziyara: (minti 4) Ka soma da bin bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Sai ka canja gabatarwarka ta yi daidai da abin da yake damun maigidan kuma ka yi amfani da nassin da ya dace. (th darasi na 12)
Jawabi: (minti 5) w08 7/1 27—Jigo: Me Ya Sa Ake Yawan Ambata Ƙabilu 12 na Isra’ila, Yayin da Ƙabilu 13 Ne Ke Akwai? (th darasi na 7)
RAYUWAR KIRISTA
“An Tsara Su don Su Yi ma Kowa Wa’azi”: (minti 10) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon nan Ka Zama Abokin Jehobah—Yin Wa’azi a Wasu Harsuna. Ka ɗan bayyana wa masu sauraro abubuwan da ke manhajar JW Language® app da aka nuna a bidiyon.
Bukatun Ikilisiya: (minti 5)
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lfb darasi na 12
Kammalawa (minti 3)
Waƙa ta 1 da Addu’a