Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

An Tsara Su don Su Yi ma Kowa Wa’azi

An Tsara Su don Su Yi ma Kowa Wa’azi

A dā, Jehobah ya tsara yadda Isra’ilawa za su masa ibada. Haka ma a yau, yana tsara bayinsa don su iya yin aikin da ya ba su. A faɗin duniya, ’yan’uwa da ke ofisoshinmu da da’irorinmu da ikilisiyoyinmu da kuma rukunoninmu na wa’azi duk suna aiki tare don su faɗaɗa aikin wa’azi. Muna ma kowa wa’azi har da waɗanda suke yin wani yare dabam. ​—R. Yar 14:​6, 7.

Shin ka taɓa yin tunanin koyan wani yare don ka taimaka wa mutanen da suke yaren su soma bauta wa Jehobah? Idan ba za ka sami zarafin koyan wani yare ba, za ka iya yin amfani da manhajar JW Language app don ka koyi gabatarwa mai sauƙi. Idan ka yi amfani da manhajar a wa’azi, za ka yi farin ciki irin wanda Kiristoci a ƙarni na farko suka yi sa’ad da mutanen wasu ƙasashe suka ji “manyan abubuwan da Allah ya yi” a yarukansu.​—A. M 2:​7-11.

KU KALLI BIDIYON NAN KA ZAMA ABOKIN JEHOBAH​—YIN WA’AZI A WASU HARSUNA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • A wane lokaci ne manhajar JW Language app za ta taimaka maka?

  • Waɗanne abubuwa ne suke manhajar?

  • Mutane daga dukan ƙabilu suna bukatar su ji albishiri

    Waɗanne yaruka ne mutanen da ke yankinku suke yi?

  • Me za ka yi idan ba ka jin yaren wani da yake son wa’azi?​—od-E 100-101 ¶39-41