KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI
Ka Taimaka wa Dalibanka Su Rika Zuwa Taro
Taron ikilisiya yana da muhimmanci a ibadarmu. (Za 22:22) Dukan waɗanda suke bauta wa Jehobah suna farin ciki kuma suna samun albarka. (Za 65:4) Ɗalibai suna samun ci gaba da sauri idan suna halartan taro a kai a kai.
Ta yaya za ka taimaka wa ɗalibanka su riƙa halartan taro? Ka riƙa gayyatarsu su halarci taro. Ka nuna musu bidiyon nan Me Ake Yi a Majami’ar Mulki? Ka bayyana musu amfanin zuwa taro. (lff darasi na 10) Kana iya gaya musu abin da ka koya a taro, ko kuma abin da za a tattauna a taro na gaba. Ka ba su littattafan da za a yi amfani da su a taron. Ka taimaka musu su halarci taron. Wataƙila suna bukatar ka je ka ɗauko su zuwa taron. Idan ka yi iya ƙoƙarinka don ka taimaka wa ɗalibinka ya halarci taro, za ka ga cewa haƙarka ta cim ma ruwa.—1Ko 14:24, 25.
KU KALLI BIDIYON NAN KU TAIMAKA WA ƊALIBANKU SU RIƘA ZUWA TARO, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Wane zarafi ne Anita ta yi amfani da shi don ta gayyaci Rose zuwa taro?
-
Me ya sa muke farin ciki sa’ad da ɗalibinmu ya halarci taro?
-
Mene ne Rose ta gani sa’ad da ta halarci taro na farko?