26 ga Fabrairu–3 ga Maris
ZABURA 11-15
Waƙa ta 139 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Ka Ɗauka Kana Sabuwar Duniya
(minti 10)
Idan mutane ba sa bin doka da oda, hakan yana jawo tashin hankali da ke koꞌina a yau (Za 11:2, 3; w06 6/1 30 sakin layi na 1)
Za mu iya kasancewa da tabbacin cewa, nan ba da daɗewa ba Jehobah zai kawar da mugunta (Za 11:5; wp16.4 11)
Yin tunani a kan alkawarin Jehobah cewa zai cece mu na taimaka mana mu kasance da haƙuri yayin da muke jiran sabuwar duniya (Za 13:5, 6; w17.08 6 sakin layi na 15)
KA GWADA WANNAN: Ka karanta Ezekiyel 34:25, sai ka yi tunani kamar kana wurin da ayar ta ambata.—kr 236 sakin layi na 16.
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
Za 14:1—Ta yaya irin halin da aka ambata a ayar nan zai iya shafi Kiristoci? (w13 9/15 19 sakin layi na 12)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) Za 13:1–14:7 (th darasi na 2)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 2) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka gayyaci mutumin zuwa taron Tunawa da Mutuwar Yesu. (lmd darasi na 5 batu na 3)
5. Fara Magana da Mutane
(minti 1) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka gayyaci mutumin zuwa taron Tunawa da Mutuwar Yesu. (lmd darasi na 3 batu na 4)
6. Fara Magana da Mutane
(minti 3) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Mutumin ya karɓi takardar gayyata zuwa taron Tunawa da Mutuwar Yesu. (lmd darasi na 7 batu na 4)
7. Almajirtarwa
(minti 5) lff taƙaitawa, bita da maƙasudi na darasi na 13. Ka yi amfani da wani talifi daga sashen “Ka Bincika” don ka taimaka wa ɗalibinka ya san yadda Allah yake ji game addinin ƙarya. (th darasi na 12)
Waƙa ta 8
8. “Hikima Ta Fi Kayan Yaƙi”
(minti 10) Tattaunawa.
Tashin hankali na daɗa ƙaruwa a duk faɗin duniya. Jehobah ya san cewa muguntar da muke gani da kuma fuskanta suna sa mu damuwa sosai. Ya kuma san cewa muna bukatar kāriya. Hanya ɗaya da yake kāre mu ita ce ta wajen Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki.—Za 12:5-7.
Hikimar da ke Littafi Mai Tsarki ta fi “kayan yaƙi.” (M. Wa 9:18) Ku yi laꞌakari da kaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da ke gaba da za su iya taimaka mana mu guji faɗawa cikin hannun mugaye.
-
M. Wa 4:9, 10—Zai dace mutum ya guji zama shi kaɗai a wurin da babu tsaro
-
K. Ma 22:3—Zai dace mutum ya dinga lura da abin da ke faruwa kusa da shi saꞌad da yake cikin jamaꞌa
-
K. Ma 26:17—Ba zai dace mutum ya sa baki a gardama da bai shafe shi ba
-
K. Ma 17:14—Zai dace mutum ya bar duk inda ya lura cewa za a yi tashin hankali. Kuma ya guji jamaꞌar da suka taru don su yi zanga-zanga
-
Lu 12:15—Ba zai dace mutum ya jefa ransa cikin hatsari don yana ƙoƙarin kāre abin da ya mallaka ba
Ku kalli BIDIYON Ku Yi Koyi da Masu Bangaskiya Ba Marasa Bangaskiya Ba—Anuhu, Ba Lamek Ba. Sai ka tambayi masu sauraro:
Ta yaya baban ya yi koyi da misalin Anuhu saꞌad da ya fuskanci taꞌaddanci?—Ibr 11:5
A wasu lokuta, Kirista zai iya ɗaukan mataki don ya kāre kansa ko abin da ya mallaka. Amma, ya mai da hankali kada ya kashe wani.—Za 51:14; ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” a Hasumiyar Tsaro na Yuli, 2017.
9. Soma Gayyatar Mutane Zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu Ran Asabar 2 ga Maris
(minti 5) Jawabin da dattijo zai bayar. Ka bayyana shirin da ikilisiyarku ta yi don jawabi na musamman da Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Ka tuna wa masu shela cewa za su iya yin hidimar majagaba na ɗan lokaci kuma su ba da awa 15 a watan Maris da Afrilu.