AYUBA 6-10
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH |Ayuba Mutum Mai Aminci Ya Nuna Takaicinsa
Ayuba ya fuskanci matsaloli kamar su talauci da ciwo mai tsanani kuma an yi masa rasuwa, duk da haka, ya kasance da aminci. Sai Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya sa shi sanyin gwiwa don ya daina bauta wa Allah. ‘Abokansa’ uku suka zo wurinsa. Da farko, sun nuna cewa sun tausaya wa Ayuba. Sai suka zauna kwana bakwai ba su ce kome ba. Bayan waɗannan kwanakin, sai suka soma masa baƙar magana da kuma zargi.
Ayuba ya kasance da aminci ga Jehobah duk da matsalolin da ya fuskanta
6:3; 7:16; 9:20-22; 10:1, 12
-
Taƙaici ya sa Ayuba yin tunanin da bai dace ba. Ya ce Allah bai damu ba ko yana da aminci ko a’a
-
Baƙin ciki bai ƙyale Ayuba ya yi tunani cewa wasu abubuwa ne suka jawo matsalolinsa ba
-
Ko da yake Ayuba yana baƙin ciki, duk da haka, ya gaya wa masu masa ba’a cewa yana ƙaunar Jehobah