RAYUWAR KIRISTA
Ku Taimaki Iyalinku Su Bauta wa Jehobah
Jehobah ya aiki Irmiya ya gargaɗi Yahudawa cewa zai halaka su domin sun daina bauta masa. (Irm 13:25) Yaya aka yi mutanen suka nisanta kansu daga bautar Jehobah? Iyalan Isra’ilawa sun yi sanyi a ibadarsu. Babu shakka, magidanta ba su bi umurnin Jehobah da ke littafin Kubawar Shari’a 6:
A yau, iyalai da suke son Jehobah sosai suna taimaka wa ’yar’uwa a ikilisiya su yi ƙarfi. Magidanta za su iya taimaka wa iyalinsu su bauta wa Jehobah. Ta yaya? Ta wajen yin Ibada ta Iyali a kai a kai da kuma gudanar da ita a hanya mai kyau. (Zab. 22:27) Ku amsa waɗannan tambayoyin bayan kun kalli bidiyon nan “Waɗannan Kalmomin . . . Su Zauna a Zuciyarku”
-
Ta yaya wasu iyalai suka magance ƙalubalen da suka fuskanta sa’ad da suke so su yi ibada ta iyali?
-
Waɗanne amfani ake samu don yin Ibada ta Iyali a kai a kai da kuma gudanar da ita a hanya mai kyau?
-
Waɗanne ƙalubale ne nake fuskanta wajen gudanar da ibada ta iyali kuma yaya nake so in magance su?