Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Bitrus da Yohanna suna shirya ɗakin da za su yi Idin Ƙetarewa na shekara ta 33

RAYUWAR KIRISTA

Kana Yin Shiri don Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

Kana Yin Shiri don Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

Idin Ƙetarewa na ƙarshe da Yesu ya yi yana da muhimmanci sosai. Tun da ya kusan mutuwa, yana so ya yi Idin Ƙetarewar tare da manzanninsa kuma ya kafa musu wata sabuwar idi da za su riƙa yi kowace shekara, wato Jibin Maraice na Ubangiji. Ya aiki Bitrus da Yohanna su je su shirya ɗakin da za su yi idin a ciki. (Lu 22:​7-13; ka dubi hoton da ke shafin farko.) Hakan ya nuna mana muhimmancin yin shiri don Taron Tunawa da Mutuwar Yesu da za mu yi a ranar 27 ga Maris. Mai yiwuwa ikilisiyoyi sun riga sun shirya wanda zai ba da jawabin da gurasar da ruwan inabin da dai sauransu. Amma, ta yaya kowannenmu zai yi shiri don wannan taron?

Ka shirya zuciyarka. Ka karanta kuma ka yi bimbini a kan Nassosin da za a karanta don Tuna Mutuwar Kristi. Za ka iya samun tsarin karatun a ƙasidar nan Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana​. Ban da haka ma, ƙasidar nan Taimako Don Nazarin Kalmar Allah darasi na 16 ya yi bayani dalla-dalla game da tsari na karatun. (Ka kuma duba Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu na watan Afrilu 2020.) Sa’ad da iyalai suke ibadarsu ta iyali, za su iya bincika bayanai da suka nuna muhimmancin fansar a Watch Tower Publications Index ko kuma Littafin Bincike don Shaidun Jehobah.

Ka gayyaci mutane zuwa taron. Zai yi kyau kai ma ka gayyaci mutane da yawa zuwa taron. Ka yi tunani a kan mutanen da za ka iya gayyata kamar waɗanda suke son saƙonmu da ɗalibanka na dā da abokanka da kuma danginka. Zai dace dattawa su tabbata cewa sun gayyaci waɗanda suka daina zuwa wa’azi da taro. Idan wanda ka gayyata ba ya zama a yankinku, za ka iya ganin lokaci da kuma wurin da za a yi taron a yankinsu ta wajen shiga sashen GAME DA MU da ke dandalinmu na jw.org, sai ka danna “Tunawa.”

Wane abu ne kuma za mu iya yi don mu shirya kanmu?