KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI
Ka Taimaka wa Dalibanka Su Zama Aminan Jehobah
Jehobah yana so mu bauta masa domin muna ƙaunarsa. (Mt 22:37, 38) Idan ɗalibanmu suna ƙaunar Jehobah, hakan zai taimaka musu su yi canje-canje kuma su tsaya daram sa’ad da suke fuskantar jarrabawa. (1Yo 5:3) Ƙauna da suke wa Jehobah ne za ta sa su yi baftisma.
Ka taimaka wa ɗalibanka su ga cewa Allah yana ƙaunarsu. Za ka iya tambayarsu cewa: “Mene ne wannan ya koya maka game da Jehobah?” ko kuma “Ta yaya hakan ya nuna cewa Allah yana ƙaunarka?” Ka sa su fahimci yadda Jehobah yake taimaka musu a rayuwa. (2Tar 16:9) Ka ba wa ɗalibanka misalan yadda Jehobah ya amsa addu’o’inka kuma ka ƙarfafa su su riƙa lura da yadda Jehobah yake amsa addu’o’insu. Muna farin ciki matuƙa sa’ad da ɗalibanmu suka san cewa Jehobah yana ƙaunarsu, kuma suna nuna cewa suna ƙaunarsa.
KU KALLI BIDIYON NAN KU TAIMAKA WA ƊALIBANKU SU ZAMA AMINAN JEHOBAH, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Wace matsala ce Rose ta fuskanta?
-
Ta yaya Anita ta taimaka wa Rose?
-
Ta yaya Rose ta shawo kan matsalar?