LIVING AS CHRISTIANS
Su Waye Ne Abokanka a Dandalin Sada Zumunta?
Aboki mutum ne da ka shaƙu da shi kuma kuna ƙauna da daraja juna sosai. Alal misali, Jonathan da Dauda sun soma abokantaka na kud da kud bayan da Dauda ya kashe Goliyat. (1Sam 18:1) Dukansu suna da halaye masu kyau, kuma abin da ya sa suka zama abokai ke nan. Saboda haka, ƙulla abokantaka ya dangana ne da sanin mutumin sosai. Sanin mutum yakan ɗauki lokaci kuma muna bukatar mu ƙoƙarta sosai. Amma a dandalin sada zumunta, yana da sauƙi mutane su zama abokai nan da nan. A dandalin sada zumunta, mutane sukan shirya abin da za su faɗa yadda zai yi wuya mutum ya gane ko su waɗanne irin mutane ne, sai su ɓoye ainihin halinsu. Saboda haka, yana da kyau ka san irin mutane da za su zama abokanka. Idan wani da ba ka sani ba yana so ya zama abokinka a dandalin sada zumunta, kada ka ji kamar ka yi laifi idan ka ƙi zama abokinsa. Tun da yake akwai haɗarurruka tattare da dandalin sada zumunta, wasu sun yanke shawara cewa ba za su shiga dandalin ba. Amma mene ne ya kamata ka riƙa tunawa idan ka yanke shawarar shiga dandalin sada zumunta?
KU KALLI BIDIYON NAN KA ZAMA MAI HIKIMA A DANDALIN ZUMUNTA NA INTANET, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Mene ne ya kamata ka yi la’akari da shi kafin ka rubuta saƙo ko saka hotuna a dandalin sada zumunta?
-
Me ya sa ya kamata ka zaɓi abokai da kyau a dandalin sada zumunta?
-
Me ya sa ya kamata ka tsai da yawan lokacin da za ka riƙa yi a dandalin sada zumunta?—Afi 5:15, 16